Alkalin kotun Grade 1 dake Karu a Abuja Umar Mayana ranar Litini ya yanke wa Surajo Hamza mai shekaru 34 hukuncin zama a kurkuku bayan an same shi da laifin yin lalata da wata matar aure.
Mayana ya hana bada belin Hamza yana mai cewa Hamza zai yi zaman kurkuku har sai rundunar ‘yan sanda sun kammala yin bincike a kai.
Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 4 ga Afrilu.
‘Yan sanda sun kama Hamza mazaunin Zaman Gida dake Asokoro a Abuja da laifin shiga wuri ba tare da izini ba, ji wa mutanen wurin rauni sannan da aikata zina.
Lauyan da ya kai kara Edwin Ochayi ya ce rundunar ‘yan sandan dake Asokoro ne suka shigar da kara a kotu.
Ochayi ya ce Hamza ya afka shagon wata matar aure Gloria Joseph wacce matar Pius Gwaza ne dake zama a Kiruduma Asokoro. Ko da ya afka shagon sai ya bi jikinta da karfin tsiya ya aikata abinda yake so, wato lalata da ita.
“ A halin haka ne fa mijin Gloria ya zo wurin matar sa inda ya iske hamza tare da ita. Daga nan ne ya fizgo Hamza sai suka kaure da kokuwa har ya raunata mijin gloria.
Ya ce da ya shiga hannun ‘yan sands Hamza ya tabbatar cewa ya aikata laifukan da ake zargin sa da su sai dai a kotu ya musanta aikata su.