Rundunar ‘yan sandan sirri ta Najeriya, SSS, a ranar Laraba ta sanar da cewa wasu manyan ‘yan siyasan Najeriya na kulla makarkashiyar a nada gwamnatin rikon kwarya, lamarin da ya tabbatar da wata zaman dar-dar da jitajita da ta karade kasar makonni kafin babban zaben da aka yi a watan Faburairu.
A cikin sanarwa da hukumar ta fitar ta ce sun bankado wasu shirye shirye da a wasu ke shiryawa a wurare da dama da suka hada tada zaune tsaye da kuma yin zangazanga a manyan biranen kasar domin dagula zaman lafiyar da mutanen kasa ke ciki daga nan sai gwamnati ta ayyana dokar ta baci a saka gwamnatin wucin gadi a kasar .
Kakakin rundunar SSS Peter Afunanya, ya kara da cewa sannan kuma suna shirin zuwa kotu domin samun umarnin daga alkalai su hana rantsar da sabuwar gwamnati da aka zaba, daga nan sai a nada gwamnatin wucin gadi.
” Ina so in tabbatar musu su sani cewa jami’an tsaro sun sa ido suna bibiyar abin sau da kafa. Ba za su bari wani abu mai kama da irin haka ya faru a Najeriya ba.
Idan har suka cimma burin su, ba za a iya rantsar da Tinubu sabon shugaban kasa ba a ranar 29 ga Mayu.
Afunaya ya yi gargadi da yin kira ga jami’an tsaro, lauyoyi da alkalai da ‘yan jarida a Najeriya da su maida hankali matuka sannan su kula da makircin wadannan mutane wadanda suka lashi takobin sai sun kawo cikas a kasar nan kafin a rantsar da sabuwar gwamnati ranar 29 ga Mayu domin a kafa gwamnatin wucin gadi ba ta Tinubu ba.
Idan ba a manta ba shugaba Buhari a cikin wannan mako ya bayyana cewa ya kagara ya mika mulki ga sabuwar gwamnati, yana mai cewa ko kwana daya ba zai kara ba idan wa’adin sa ya cika.