Ofishin Kula da Basussukan da ake bin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi ya tabbatar da cewa kafin shekarar 2022 ta ƙare, bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 46.25.
Adadin ya nuna cewa bashin ya ƙaru da kashi 14.46 tsakanin Disamba 2021 zuwa Disamba 2022.
Ofishin ya ce a ranar ƙarshen 31 Ga Disamba, 2021 bashin da ake bin Najeriya Naira tiriliyan 39.56 ne.
Adadin Naira tiriliyan 46.25 ɗin da ake bin Najeriya bashi na daidai da dala biliyan 103.11 a ƙarshen Disamba,. 2022.
Adadin tulin bashin ya ƙunshi na cikin gida da na waje da gwamnatin tarayya, jihohi 36 da FCT Abuja su ka ciwo.
Ofishin Kula da Basussuka, wato DMO ya ce basussukan cikin gida sun kai Naira tiriliyan 27.55, sai kuma Naira tiriliyan 18.70 basussukan daga waje.
Dalili ƙatuwar bashin daga Disamba 2021 zuwa Disamba 2022 shi ne bashin da aka riƙa ciwowa domin a yi ayyukan cikin kasafin kuɗi.
Tulin Basussuka: Yadda Alƙaluman DMO su ka Kunyata Wani Hadimin Buhari:
Cikin watan Nuwamba, 2022, wani hidimin Shugaba Buhari ya yi iƙirarin cewa, “ana yin ƙarin gishiri a labaran tulin bashi da taɓarɓarewar tattalin arzikin Najeriya
Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Jama’a, Ajuri Ngelale, ya kare mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce masu yawan sukar tulin bashin da ake bin Najeriya su na ƙarin gishiri sosai.
An tattauna da shi a Gidan Talbijin na Channels, a ranar Alhamis.
Ya ce akwai ƙarin gishiri sosai a cikin bayanan tulin bashin Naira tiriliyan 41 da ake cewa ana bin Najeriya.
Buhari ya hau mulki a bisa alƙawarin “CHANJI”, amma kuma sama da shekaru bakwai kenan bayan hawan sa mulki, ba a samu canjin da ake tunanin samu ba, ballantana a ce an cika alƙawarin da aka daukar wa talakawa.
An samu tsadar rayuwa, tashin farashin kayan abinci, kama daga kayan gona har zuwa kayan masarufi.
Akwai matsalar tulin bashi da rugurgujewar darajar Naira.
Kafin saukar PDP daga mulki dai Dalar Amurka ɗaya na daidai da naira 197. Amma a yanzu ta haura 870.
Yayin da bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 41.62, Najeriya ta na biyan kusan ilahirin kuɗaɗen shigar ta wajen biyan basussuka, kuma hatta ma kasafin 2023 sai an ciwo bashin naira tiriliyan 8.2 sannan a iya gudanar da shi.
Kada a manta, bashin da PDP ta sauka ta bari, na naira tiriliyan 12.6 kaɗai.
Duk da haka, Ngelale wanda mataimakin Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Bola Tinubu ne, ya ce APC ta fi PDP ƙoƙartawa, sannan kuma idan mutane su na batun yawan basussukan da Gwamnatin Buhari ta ciwo, ba su yin la’akari da cewa an yi ayyukan raya ƙasa ne waɗanda kowa zai iya gani a fili.