TAMBAYA: Matan da mijin ta ya tilasta ta suka sadu suna azumin Ramadan, za ta yi Kaffara ko A’A?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Subhana Lillah! Yin jima’i da rana a cikin ramadana laifi ne mai girma da ya shafi matan da mijin baki daya, kuma keta alfarman ramadana ne, yin haka sabawa Allah ne, wajibe ne ku Tuba zuwa ga Allah.
Wannan saduwar ta bata azumin su (matan da mijin baki daya), sannan za su cigaba da kame baki, kuma za su rama wannan azumin. Kaffara ta wajaba akan wannan mijin.
Amma matar babu kaffara akanta sai dai idan ta biye masa ba akan tilas ba. To, itama za tayi kaffara, don ta mika kanta zuwa ga sha’awarta. Amma idan ya tilastamata ko ya tursasamata, to, babu kaffara akan ta.
Allah she ne mafi sani.
TAMBAYA: Shin Dagaskene Ana ninka laifi kamar yadda ake ninka Lada a watan ramadan?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Babu shakka a cikin girma da Alfarman watan Ramadan, watane da ake nisantan muyagun laifuka manya da kanana, kuma ake rige-rige cikin ayyukan kwarai, watane da ake ‘yanta bayi daga wuta.
Amma laifi a cikin Ramadana yafi tsananin zunubi da girman ukuba fiye da laifi a cikin watan da ba shi ba, don zunubin sabo yana kara girma da muni idan aka aikata shi a wani wuri ko lokaci na musamman. Kamar yadda aikin kwarai yake kara lada da daraja a lokuta da gurare na musamman.
Milasali: mutumin da ya yi satan takalmi a masallaci da wanda ya yi a kasuwa duk barayi ne. Amma a ganinka wane barawon ne satar sa tafi muni?
Discussion about this post