Kotun Grade 1 dake Karu a Abuja ta bada belin Nafisa Abbas akan naira 100,000 bisa laifin kwarara wa makwabciyarta tafashen ruwan wake daga murhu ta kwarara mata.
Alkalin kotun Umar Mayana ya ce Nafisa za ta gabatar da shaidu biyu wanda za su gabatar wa kotun katinsu na shaida da adireshinsu da kotu za ta iya tabbatar wa.
Mayana ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 28 ga Maris.
Lauyan da ya shigar da karan Olanrewaju Osho ya ce rundunar ‘yan sanda sun gurfanar da Nafisa bisa laifin ji wa ‘yar uwanta mace rauni a jiki da kuma tada hankalin mutanen unguwa.
Osho ya ce wata rana makwabciyar Nafisa ta shiga dakin dafa abincin Nafisa domin ta debi ruwa zafi ta yi wa ‘yarta wanka.
“Garin debo ruwan ne Nafisa ta hango ta shine fa ta zuba da gudu ta suntumi tafashen wake da ke kan murhu tana dafawa ta sheka mata a jiki.
Dukkan su suna zama ne a gida daya, wato gidan haya.
Discussion about this post