Shugaban cocin ‘Church of Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry’ dake Sabon Tasha, Kaduna fasto Yohannan Buru ya ce cocin ta raba kayan abinci da kudi a babban masallacin dake Kano Road domin domin taimaka wa musulmai matalauta da abincin da za su rika yin buda baki da sahur a lokacin azumin watan Ramadana.
Musulmai a fadin Najeriya za su fara yin Azumin watan Ramadana ranar Alhamis, 23 ga Maris.
Butu ya ce babban dalilin da ya sa cocin sa ta ke yin haka musammam a wannan lokaci shine don ganin irin tsananin da aka shiga a kasar da kuma wahalar man fetur da ake yi.
Ya ce a shekarar bara cocin ta raba abinci gabanin Ramadan a jihohi biya a kasar nan.
“Bana cikin kayan da muka raba mun hada da butoci da tabarmi domin karfafa wa Musulmai yin ibada da addu’o’i domin Allah ya kawo mana saukin matsalolin da muke fama da su a kasar nan.
“ A wannan shekarar burin mu shine mu tallafawa akalla Musulmai 1,000 da nauin abinci daban-daban.
Daya daga cikin shugabanin kungiyar nakasassu Malan Hassan Mohammed ya mika godiyarsa ga cocin yana mai cewa cocin na yin irin haka shekaru 30 kenan da suka wuce kuma har yanzu bata fasa ba.
Bayan masakai da matalauta, cocin ta raba wa wasu makarantun allo abincin domin wannan watan.
Discussion about this post