Fasto Chukwuemeka Ohanere da aka fi sani da Odumeje ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai mutu saboda ya kammala aikinsa a duniya.
Shugaban cocin ‘Mountain of Holy Ghost Intervention Dan Deliverance Ministry’ dake Fagge a Onitsha jihar Anambra ya fadi haka ne a cocinsa ranar Lahadi.
Odumeje ya ce ya kira babban dansa mai suna King David ya sanar da shi cewa zai mutu nan ba da dadewa ba sannan hakkin kula da kannen sa da mahaifiyar su ya rataya a kansa bayan ba shi nan.
“Na zo duniyan nan da don in aiwatar da wani abu ne kuma yanzu na kammala tsaf saboda haka zan sheka lahira nan ba da dadewa ba.
A shekarar bara wasu jami’an gwamnatin Anambra suka lakada masa dukan tsiya bayan zarginsu da ya yi wai sun zo su rusa masa coci.
Fasto Odumeje ya dade yana fafatawa da bokaye kan ikon da suke da shi na yin mu’ujiza.
Yana da shekaru 40 a duniya.