Mu dai fatan mu, da addu’ar mu, da rokon Allah mu shine, Allah ya bamu shugabanni na kwarai, nagari, wadanda zasu zama alkhairi ga Musulunci, gare mu, ga Nigeria, da ‘yan Nigeria, ga arewa, da ‘yan arewa da kuma al’ummah baki daya, amin.
Ko Muslim-Muslim, ko Muslim-Christian, duk daya ne. Duk wanda mutum yayi ra’ayi ya zaba yayi daidai, bai sabawa Allah ba, bai yi zunubi ba, bai yiwa kowa laifi ba.
Su Babachir, da su Dogara, da kuma masu kokarin Musuluntar da Muslim-Muslim, su kafirtar da Muslim-Christian, wadannan duk domin kan su suke yi, domin ra’ayinsu suke yi, ba domin al’ummah ba!
Sam bai kamata addinin Allah ya zama abun wasa ba. Bai kamata mu kawo maganar addini muna haddasa rikice-rikice da tashe-tashen hankula da zubar da jinin bayin Allah a cikin al’ummah ba!
Addinin Allah ya zama bai da wata daraja sai an zo maganar siyasa, sai muyi kokarin amfani da shi domin cimma wasu manufofinmu?
Wallahi muji tsoron Allah. Kar mu yarda mu bayar da gudummawa wurin kara rugujewar arewa.
Magabatan mu ba haka suka yi ba wallahi.
Kuma mu sani, arewa ba abunda ya rage muna sai mulkin nan, idan kuma muka yi sakaci, to ya rage namu…!
Allah ya jikan magabatanmu, amin.
MU HADU MUYI DUK ABUNDA ZAMU YI, AMMA KOWA YASAN GIDAN UBANSA!
Kuma Dan uwana ka sani, wannan ra’ayi nane, kuma fahimta tace, kai ma ban hana ka kayi naka ra’ayin ko taka fahimtar ba!
Allah yasa mu dace da shugabanni nagari, amin.
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau
Alhamis, 02/02/2023.
Discussion about this post