Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za su fallasa masu yi wa takarar Bila Tinubu zagon ƙasa a fadar shugaban kasa.
El-Rufai ya ce, mun san su kuma za mu fallasa su. Sun yake mu a lokacin zaɓen APC kuma duk mun kada ƴan takarar su, haka suka zo mana da wata sabuwa suka nada wani ya ƙalubalance mu a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa, a nan ma muka ti rugurugu da su. Shine kuma yanzu suka bijiro da da waɗannan dabaru don APC ta faɗi zaɓe.
” Dukkan su da ke yi mana zagon sa ba su da tasiri a wuraren su da mutanen su. Karfin su dai a fadar shugaban kasa yake. Ni na yi takara sau biyu kuma na samu Kuri’u sama da miliyan wanda da su na ci zabe. Su ko ba za su iya ba don ba su da kima a idanun mutanen su.
” Muna nan muna aiki tukuru don ganin mun yi nasara a zaɓen shugaban kasa da za a yi nan da sati uku, kuma inshaAllah za mu yi nasara a zaɓen. Idan Tinubu ya yi nasara za mu bankaɗo waɗannan kadangarun dake neman hana ruwa gudu.
Idan ba a manta ba gwamna El-Rufai ya bayyana a hira da talabijin din Channels da yai cewa akwai wasu makusantan Buhari da ke yi wa takarar Tinub zagon kasa, waɗanda ke tursasa bijiro da wasu abubuwa domin APC ta faɗi zabe a 2023.