Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Bola Tinubu, ta yi gargaɗi da roƙo ga manoman Najeriya cewa kada su zaɓi ɗan takarar da ke da niyyar idan ya zama shugaban ƙasa zai buɗe kan iyakokin Najeriya.
Daraktan Harkokin Noma na kamfen ɗin Tinubu, Abubakar Bello ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da kungiyoyin manoma a Hedikwatar APC da ke Abuja.
Bello ya ce kada manoma su yi fargar jajin zaɓen wanda idan ya hau mulki zai maida hannun agogon ayyukan bunƙasa noma da wannan ta yi a baya.
“Kada mu yi sakaci, sagegeduwar tafka kuskuren da zai kai mu ga samun shugaban da idan ya hau sau buɗe kan iyakokin Najeriya ta ƙasa. Saboda mun gani a labarai wani ɗan takarar shugaban ƙasa na cewa idan ya yi nasara zai buɗe kan iyakokin Najeriya. To me wannan abu zai haifar wa ‘yan Najeriya kenan?
“Za shi maida mu shekarun baya, lokacin da shinkafa ma sai an shigo mana da ita daga waje. Haka makamai, kuma matasan mu za su rasa aikin yi kenan. Dukkan masana’antun shinkafa za su mutu kenan fa murus. Don haka mu tashi mu wayar da kan mambobin mu domin a zaɓi Tinubu.”
Tun cikin 2019 Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakokin Najeriya da nufin daƙile sumogal.
An buɗe wasu kan iyakokin cikin 2021, amma kuma an haramta shigo da shinkafa, kayan kiwon kaji da sauran su.
Sai dai kuma maimakon a samu sauƙin kayan abinci, sai farashin sa ya nunka nunkin-ba-nunkin, har talakawa na kukan cewa har ma gara lokacin da kan iyakokin ke buɗe, abincin ya fi sauƙin farashi a lokacin.
Discussion about this post