Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano da kanawa gaba dayan su sun gama shiri tsaf domin yi wa shugaban kasa Buhari kyakkyawar tarba a Kano ranar Litinin.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Kano ranar Litinin domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.
Ganduje tare da makarraban sa da suka hada da Sanata Barau Jibrin da Sanata Kabiru tare da wasu manyan jami’an gwamnati sun yi tattaki har zuwa garin Daura domin ganawa da Buhari.
Bayan ganawar su da shugaban Buhari, Ganduje ya bayyana wa manema labarai a Daura cewa sun yi tattaki ne zuwa wurin Buhari domin su roke shi a kara tsawon wa’adin canja takardun kudi da zai kare ranar 31 ga Janairu.
” Mun sanar wa Buhari irin yawan ‘yan kasuwan dake Kano da kuma karancin bankuna da ake fama da su a karkara. Ya saurare mu kuma ya gaya mana cewa an kara wa’adin ranakun ajiyar kudin sannan kuma an umarci bankuna su kara yawan kudaden da suke rabawa mutane musamman yan kasuwa.
” Jihar Kano ce jiha da tafi yawan mutane a kasar nan. Sannan kuma jihar ce aka fi hadhadar cinikayya da takardun kudi. Legas ta fi kano ci gaba a harkar kimiyya saboda haka ba za su kasance cikin matsin da mutanen mu ke ciki ba.
” Akwai kananan hukumomi 24 da basu da da banki ko da daya a Kano dalilin da ya sa abin ya zo mana da matsaloli kenan.
A karshe ya godewa shugaba Buhari kan sauraran su da yayi da kuma kara wa’adin canja kudin da jiye tsoffin kudi a bankuna.