Kotun shari’a dake jihar Kano ta yanke wa Alkasim Murtala mai shekara 25 hukuncin bulala biyar bayan an kama shi da laifin satar mudun dabino hudu.
Kotu ta gurfanar da Murtala mazaunin kwatas din Koki dake Kano bisa laifuka biyu da suka hada da shiga wuri ba tare da izini ba sannan da sata.
A hukuncin da ya yanke wa Murtala alkalin kotun Malam Ismai’l Muhammad-Ahmed ya baiwa Murtala zabin zama a kurkuku na tsawon wata daya ko ya biya taran Naira 5,000 tare da yi masa bulala biyar.
Dan sandan da ya shigar da kara, Abdullahi Wada ya ce wani Ahmed Malamai ne ya kawo karar abin da Murtala ya aikata ranar 24 ga Janairu a ofishin ‘yan sanda dake Fagge.
Wada ya ce a ranar Murtala ya saci mudu hudu na dabino da kudin sa ya Kai 10,000 a shagon Malami dake kasuwar Sabon Garin Kano.
Discussion about this post