Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar Kogi Enimola Eniola ya aika wa sarkin Okene, Ohinoyi na kasar Ebira korafi bisa zargin rashin mutunta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Yahaya Bello.
Wasikar wanda Eniola ya aika wa basaraken ranar 5 ga Janairu ta umarci Ohinoyi Ado Ibrahim ya amsa wasikar cikin awa 48 yayi bayani dalla-dalla dalilin da ya sa ya gurza wa shugaban Kasa rashin mutunci da gwamnan na kin fitowa a lokacin ziyarar sa jihar.
Idan ba a manta ba shugaba Buhari ya ziyarci jihar Kogi a makon jiya inda ya ƙaddamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ta yi.
Cikin ayyukan harda ƙawata ginin fadar sarki Ohinoyi na Ebira.
Sai dai kuma Ohinoyi Ado Ibrahim bai fito ya tarbi gwamna Bello da Buhari ba a lokacin ziyarar.
Gwamnatin Kogi ta ce da gangar Ohinoyi ya ki fitowa wurin wannan taro don ya wulakanta gwamnan sannan ya da nuna rashin mutunci ga shugaba Buhari.
” Abinda da kayi na rashin biyayya da rashin mutunta babban bakon mu, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai iya sanya wa yankin Ebira bakin tawada a idanuwar mutane.
” Abin da ka yi zai sa arika wa Ebiri ganin ba mutanen kirki bane, ba su mutunta baki musamman shugaban kasa wanda shine mutum n farko a ƙasarnan.
” Ka wulaƙanta gwamna a gaban shugaban kasa, ka ki fitowa da gangar duk da sanar da kai da aka yi lokaci mai tsawo kafin ziyara shugaban kasa.
Discussion about this post