Ɗan majalisan dokokin jihar Kano dake wakiltar Gwale a majalisa Yusuf Babangida ya komo APC daga NNPP, jam’iyyar da ya koma a baya.
Babangida jigo ne kuma makusancin jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma ɗan takaran shugaban kasa na NNPP Rabiu Kwankwaso.
“Ni da na koma NNPP na ɗauka ana tare ne. Za a bi doka sannan a yi tafiya da kowa da kowa, ashe marmari ne daga nesa.
” Ɗauki ɗaiɗai ake yi a jam’iyyar, idan ba ana yi da kai bane ko kula ka ba ayi. Ba a binnka’idojin jam’iyya, duk inda masu faɗi a ji a jam’iyyar suka karkata nan ne za a bi ka kana so ko baka so.
Honarabul Babangida ya ce ba zai iya zama a irin wannan jam’iyya ba shine ya sa ya ga gara dai ya dawo APC kawai inda ya fi gane lissafin sa.
Discussion about this post