Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa Sojojin Najeriya da ke yaƙin kakkaɓe ta’addanci, sun kashe ‘yan Boko Haram da ISWAP 40 a cikin makonni biyu.
Wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Musa Ɗan makami ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an kuma samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’addar har su 47 a cikin makonnin biyu.
“An samu wannan nasara daga ranakun 17 zuwa 24 Ga Nuwamba, sannan kuma an kama wani gogarman da ke wa Boko Haram jigila da safarar makamai da kayayyakin buƙatu na yau da kullum.” Inji Ɗanmadami.
Ya ce mai jigilar makaman an kama shi ne a wurin shingen bincike na sojoji a Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Barno.
“An kashe Boko Haram da ‘yan ISWAP musamman a yankin Mallam Fatori da Tumbun Filani.
Ya ƙara da cewa Sojojin Najeriya za su ci gaba da ƙara himma da azama har sai sun kakkaɓe Boko Haram a cikin ƙasar nan.
Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 40, an damƙe 47 har da mai masu jigilar abinci da makamai.
Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa Sojojin Najeriya da ke yaƙin kakkaɓe ta’addanci, sun kashe ‘yan Boko Haram da ISWAP 40 a cikin makonni biyu.
Wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Musa Ɗan makami ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an kuma samu nasarar cafke wasu ‘yan ta’addar har su 47 a cikin makonnin biyu.
“An samu wannan nasara daga ranakun 17 zuwa 24 Ga Nuwamba, sannan kuma an kama wani gogarman da ke wa Boko Haram jigila da safarar makamai da kayayyakin buƙatu na yau da kullum.” Inji Ɗanmadami.
Ya ce mai jigilar makaman an kama shi ne a wurin shingen bincike na sojoji a Ƙaramar Hukumar Bama ta Jihar Barno.
“An kashe Boko Haram da ‘yan ISWAP musamman a yankin Mallam Fatori da Tumbun Filani.
Ya ƙara da cewa Sojojin Najeriya za su ci gaba da ƙara himma da azama har sai sun kakkaɓe Boko Haram a cikin ƙasar nan.
Discussion about this post