Tsohon shugaban hukumar cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji ya bayyana yadda wasu jami’an tsaro na sirri suka dira gidan sa suka kusa sace da karfin tsiya.
Magaji ya ce ” Wasu jami’an tsaro da suka badda kama sun yi kokarin sace shi ranar Laraba da yamma, sai dai hakar su bai cimma ruwa ba domin mutanen unguwa sun dira musu, inda suka hana su arcewa da Muhuyi, sai sai su yagalgala masa jamfar sa.
Sai dai kuma Shugaban hukumar wanda ya gaji Magaji Balarabe Mahmud, ya ce an aiko jami’an tsaro ne su gudanar da sintiri, shawage da duba gari a yankin gidan Magaji, ba kamashi aka aika su yi ba.
Idan ba a manta ba tun bayan dakatar da Magaji da gwamnantin Abdullahi Ganduje ta yi, ya ke ta fuskantar barazana daga gwamnati ba tun yanzu ba.
Discussion about this post