Ko ta wace fuska, kusurwa makaifa ka kalli manyan jam’iyyu biyu daga cikin masu tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, za ka ga cewa duk kalar su ɗaya, irin su ɗaya kuma mutanen su ma ɗaya. A nan ana magana ne a kan APC da PDP. Idan mai karatu ya kai ƙarshen wannan rubutun, kawai zai gane cewa ba wani tseren inganta dimokraɗiyya ne za a yi ba, kawai dai tseren tsere wa talakawa za a fafata a 2023.
Mu je zuwa – wai mahaukaci ya hau kura, sai a fara sukuwa.
SUKUWAR 2023: Jerin Shugabannin APC Waɗanda Tsoffin ‘Yan PDP Ne.
1. Shugaban APC Abdullahi Adamu, tsohon ɗan PDP ne. Ya yi gwamnan PDP shekaru takwas a Jihar Nassarawa.
2. Sakataren APC na Kasa, Iyiola Omisore, tsohon ɗan PDP ne.
3. Betta Edu, Shugabar Matan APC, tsohuwar ‘yar PDP ce.
4. Mashawarcin APC Ɓangaren Shari’a, Barista Ahmed El-Marzuk tsohon ɗan PDP ne.
5. Ma’ajin Kuɗaɗen APC na Ƙasa, Matthew Ofika, shi ma tsohon ɗan PDP ne.
6. Mai Binciken Kuɗaɗen APC, Sanata Abubakar Maikafi, tsohon ɗan PDP ne.
7. Sakataren Walwalar APC na Ƙasa, F.N Nwosu shi ma tsohon ɗan PDP ne.
8. Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu maso Gabas, Emmanual Enuku, shi ma tsohon ɗan PDP ne.
9. Mataimakin Shugaba Reshen Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, shi ma tsohon ɗan PDP ne.
10. Mataimakin Sakatare na Kasa, Barista Festus Fuanter, shi ma tsohon ɗan PDP ne.
SUKUWAR 2023: Jerin Shugabannin PDP Waɗanda Tsoffin ‘Yan APC Ne:
1. Iyorchia Ayu Shugaban PDP, da shi aka kafa APC, bayan ficewar sa daga PDP zuwa AC sannan sai APC.
2. Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, shi ma tsohon ɗan APC ne. Da shi aka kafa jam’iyyar ma.
3. Taofiq Arapaja, Mataimakin Shugaban PDP na Kudu, tsohon ɗan APC ne.
4. Umar Damagum, Mataimakin Shugaban PDP na Arewa, tsohon ɗan APC ne.
5. Samuel Anyawu, Sakataren PDP na Ƙasa, tsohon ɗan APC ne.
6. Ahmad Mohammed, Ma’ajin PDP na Ƙasa, tsohon ɗan APC ne.
7. Umar Bature, Sakataren Tsare-tsaren PDP na Ƙasa, tsohon ɗan APC ne.
8. Kamaldeen Abdullahi, Mashawarcin PDP a Fannin Shari’a, tsohon ɗan APC ne.
9. Ibrahim Abdullahi, Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai, shi ma tsohon ɗan APC ne.
10. Hajara Wanka, Mataimakiyar Shugabar Matan PDP, ita ɗin ma tsohuwar ‘yar APC ce.
Discussion about this post