Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya yi barazanar yi koma menene a zaɓen 2023 don ganin APC ta kafa gwamnati a jihar Kano.
Abbas ya bayyana haka ne a wurin taron jam’iyyar da aka yi a karamar hukumar Gaya.
Sai dai kuma wasu da dama daga cikin ƴan siyasan Kano, sun bayyana kalaman ta sa a matsayin barazana da kuma ganganci.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, Honarabul Shaaban Sharaɗa ya yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta kama Abbas bisa waɗannan kalamai da yayi.
” Irin waɗannan kalamai za su iya tada zaune tsaye a jihar Kano. Mutum irin sa ya furta haka, kamata yayi jami’an tsaro su gaggauta damke shi maza-maza.
Jihar Kano na daga cikin jihohin da za a gwabza tsakanin ƴan takara da ake ganin suna da karfin gaske a jihar.
Baya ga Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC, akwai Abba Gida Gida, na Jam’iyyar Kwankwaso, wato NNPP, sai kuma Wali na PDP da kuma Sharada na ADP.
Discussion about this post