Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da cewa hare-haren banka wa ofisoshin ta wuta a wasu sassan ƙasar nan ba zai hana gudanar da zaɓen 2023 ba.
Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya tabbatar da haka a lokacin da tawagar Jami’an Duba Shirye-shiryen Zaɓe na Ƙungiyar Haɗin Kan Afrika, AU su ka kai masa ziyara a ranar Litinin, a Abuja.
Da ya ke bayyana masu abubuwan da su ka faru cikin makonni uku da su ka gabata, Yakubu ya ce “INEC za ta sake samar da dukkan kayan da aka lalata a hare-hare uku da aka kai wa ofisoshin INEC na jihohin Ogun, Osun da Ebonyi.
“Makonni uku da su ka gabata an kai wa ofisoshin INEC hari, aka banka masu wuta a wasu yankunan ƙasar nan. An lalata wasu kayayyakin zaɓen 2023 da INEC ta fara rarrabawa a ƙasar nan. Amma kuma hakan ba zai hana wannan hukumar gudanar da zaɓen 2023 ba.
“Sannan kuma duk da wannan lamarin abin damuwa ne matuƙa, to wani abin farin cikin shi ne INEC za ta maye dukkan kayan zaɓen da aka lalata,” inji Yakubu.
Wannan jarida ta bada labarin cewa an sake banka wa ofishin INEC wuta a Ebonyi.
Wasu ‘yan ta-kife sun bi dare sun banka wa ofishin Hukumar Zaɓe INEC wuta a Jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a Najeriya.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ne ya tabbatar da faruwar lamarin, cikin wata sanarwar da ya fitar.
Okoye ya ce ofishin da aka bi dare aka banka wa wutar ya na garin Iboko, cikin Ƙaramar Hukumar Izzi.
Ya ce maharan sun banka wa ofishin wuta wajen ƙarfe 10 na dare, inda aka yi asarar kayayyakin zaɓe masu yawan gaske.
Duk da cewa Okoye ya tabbatar da cewa an ƙone katinan rajistar masu zaɓe, amma bai tantance adadin ko nawa su ka salwanta ba.
Ya kuma ƙara da cewa Kwamishinan Zaɓe ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi ce ta sanar da hedikwatar INEC a Abuja.
“An yi asarar kaya masu yawan gaske, waɗanda su ka haɗa akwatinan zaɓe 340, akurkin shiga a dangwala ƙuri’a guda 130, janareto mai aiki da wuta guda 24 da kuma manyan tankunan zuba ruwa da wasu kayayyaki da yawa.
Discussion about this post