Shugaban NNPC Limited, Mele Kyari ya fallasa cewa rayuwar sa na cikin hatsari, wasu gaggan da canje-canjen da ya ke yi a kamfanin man bai yi masu daɗi ba, su na barazanar kashe shi.
Kyari ya bayyana haka ranar Laraba, Taron Bitar Ƙa’idoji da Bin Diggigin Ayyuka wanda Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta shirya.
Kwamitin Yaƙi da Rashawa da cin hanci na Majalisar Wakilai ta Ƙasa ne ya shirya taron.
Ya ce masu adawa da canje-canjen da ake samu a fannonin fetur sun koma su na yi masa barazanar kashe, domin ya hana su yin abin da su ka ga dama.
“Ba tare da na tsaya kame-kame ba, ina so na bayyana cewa wannan fanni na ya na fuskantar babbar barazana. Akwai gagarimin sauye-sauye, waɗanda sakamakon hakan barazana ce ga mutane da dama, ciki har da ni.
“Ana yi wa rayuwa ta barazanar kisa. Na samu barazanar kisa da dama, amma duk da haka ba mu damu ba, saboda mun yi amanna cewa kushewar baɗi sai baɗi.
“Mun yi imani cewa babu wanda zai mutu sai lokacin mutuwar sa ya yi.
“Ba wani abu ya haifar yi mana wannan barazanar ba sai canje-canjen da mu ke yi. Kuma idan mutane su ka fita daga wani kadarko su ka shiga wani sabon yanayi wanda aka toshe masu hanyar da su ke amfana, to za su harzuƙa,” inji Kyari.
Daga nan ya ce ba laifin NNPC ba ne da ake sumogal ɗin fetur. Ya ce matsawar dai za a riƙa aikata na daidai ba, to sumogal ba zai taɓa raguwa ba.
Ya ce ba za a ɗora wa NNPC laifin sumogal ɗin fetur da kuma wasu matsalolin daban.
“A wasu wurare gwamnati na biyan tallafin fetur har naira 290 a kowace lita ɗaya fetur.
Dangane da kasa riƙa tura cinikin da fetur a Asusun Bai Ɗaya na Gwamnatin Tarayya, Kyari ya ce a yanzu ƙasar nan ba za ta iya tsayar da farashin bai ɗaya.
Discussion about this post