Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa yara biyu cikin biyar din da mahaifinsu ya banka wa wuta sun mutu.
Kakakin rundunar Funmilayo Odunlami wacce ta sanar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Talata ta ce yaran sun mutu a dalilin kunan da suka yi.
Funmilayo ta ce likitocin asibitin FMC Owo na kokarin ceto sauran yaran.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahaifin yaran mai shekara 54 Joseph Ojo ya cinna wa ‘ya’yan sa biyar wuta a gidan sa dake Fagun crescent a garin Ondo.
Sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna c Ojo ya duldula wa yaran fetur yayin da suke barci sannan ya kesta ashana.
Daya daga cikin yaran ya mutu a hanyar zuwa asibiti.
Wani da abin ya faru a idon sa da baya so a fadi sunnan sa ya ce Ojo ya aikata haka ne saboda rashin jituwan da ya shiga tsakaninsa da matarsa.
Ya ce a wannan ranar Ojo ya so yin jima’i da matar sa amma sai ta ki bashi hadin kai kuma dama can ta dade tana kaurace masa.
Matar da Ojo ya aura bazawara ce da ta haifi ‘ya’ya biyar a aurenta na fari.
Bayan ta auri Ojo sai ta haifi ‘ya biyu wanda a yanzu haka sun kai wata 18 da haihuwa.
Funmilayo ta ce da zaran rundunar ta kammala gudanar da bincike za ta kai Ojo kotu domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post