Kwamitin dattawan jam’iyyar PDP karkashin shugabancin Tsohon shugaban majalisar dattawa Adolphus Wabara ta umarci shugaban jam’iyyar, Iyorchia Ayu da ya yi alkawarin zai sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar bayan zaɓen 2023.
Wabara ya ce kwamitin ta yanke wannan shawara ce saboda akao karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa a jam’iyyar ta PDP.
Wabara ya kuma umarci ƴaƴan jam’iyyar gaba ɗaya su daina faɗin kalaman da za su iya wargaza jam’iyyar maimakon haɗin kai da ake so domin tunkarar zaɓen 2023.
Bayan haka, Wabara ya ƙaryata, raɗeradin da ake ta yaɗawa wai jam’iyyar ta dakatar da kamfen ɗin ta.
Shugaban kwamitin kamfen ɗin shugaban kasa na PDP Gwamna Aminu Tambuwal, ya ce PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar za su dira garin Kaduna ranar Litinin.
Harƙallar Iyorchia Ayu – Ayu
Gwamna Nyesom Wike ya saƙe zargin Shugaban PDP Iyorchia Ayu da hannu cikin yin rub-da-ciki kan wasu maƙudan kuɗaɗen kwangila.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida yau Juma’a a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, Wike ya yi zargin cewa Ayu ya karɓi kuɗaɗen wata kwangila ta PDP har sau biyu, abin da a Turance ake kira ‘double payment’.
“,Idan mu ka ƙara fallasa harƙallar Ayu da ke a hannun mu, su kan su ‘ya’yan sa sai sun ce masa kai ba mahaifin mu ba ne” inji Wike.
Kwanakin baya ne kuma Wike ya yi zargin cewa wani ɗan takarar gwamna a PDP ya ba shi toshiyar baki ta naira biliyan ɗaya, kafin zaɓen fidda gwanin PDP da aka yi cikin Mayu.
Da aka tambaye shi me ya sa har yanzu Ayu bai yi masa raddi ba, sai Wike ya ce, “Ai ba shi da bakin yin wata magana. Ba zai iya cewa komai ba.
“Kai bari ma ku ji wata sabuwa. Ayu ya karɓi naira miliyan 100 wajen wani gwamna da sunan zai yi wa cibiyar dimokraɗiyya ta PDP kwaskwarima. Bayan ya karɓa, sai kuma ya kewaya ya sake karɓar naira miliyan 100 a hannun Kwamitin Zartaswar PDP da sunan zai yi wancan aikin.”
Wike ya ƙalubalanci Ayu ya fito idan ya isa ya ƙaryata shi. Ya ce shi kuma daga nan zai fallasa shi, ya baje komai a faifai don kowa ya gani.
“Tilas shugaba ya kasance nagari abin kwatance kuma abin koyi. Amma an ɗora mutum maras nagarta wai shi zai jagoranci kamfen ɗin da za a kafa gwamnati,” cewar Wike.
A wurin tattaunawar, Wike ya sake shaida wa manema labarai cewa Ayu ya yi masu alƙawarin cewa zai sauka daga muƙamin sa a naɗa ɗan Kudu, matsawar dai ɗan Arewa ne aka zaɓa matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.
Ayu ya ce muƙamin da aka bai wa Gwamna Ifeanyi Okowa na mataimakin takarar shugaban ƙasa ba wata tsiya ba ce.
Ya ce bai yiwuwa a ce ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma shugaban jam’iyya su fito daga shiyya ɗaya. Wannan rashin adalci ne. Saboda haka ya ce a bai wa kudu muƙamin shugaban jam’iyya, tunda ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga Arewa.
“Ba zai taɓa yiwuwa ba a danne wa mutane na haƙƙin su kuma a ce na ƙi yin magana, sannan kuma a ce ana son ƙuri’un su.
“Tunda ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga Arewa, to shugaban PDP ya sauka a bai wa ɗan kudu, ko ma daga wace jiha ce, in dai a kudun ne.” Inji Wike.
Discussion about this post