Ƴan bindiga sun sace hakimin Birnin Tsaba Alhaji Hashimu dake jihar Zamfara
Alhaji Hashimu ma’aikacin jami’an Jami’ar gwamnatin Tarayya dake Gusau.
Bayan Hashimu da aka sace, sun ɗauke wani ɗalibin jami’ar.
Wani mazaunin Zurmi ya bayyana wa wakilin mu cewa ƴan bindigan sun nemi a hiya su naira miliyan 5 da wasu mashina biyu da jami’an tsaro suka kwace a hannun wasu ƴan bindiga da aka cafke a lokacin da suke kokarin shiga da su cikin daji.
Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa suna biyayya ga gogarman Dan Karami, wanda shine ke iko da dazukan kewayen Zurmi (jihar Zamfara) da Jibia (jihar Katsina).
” Shi Alhaji Hashimu na taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri game da ƴan bindiga. Sun daɗe suna neman sa. Jami’an tsaro sun kama wasu mashina biyu wanda za akai su cikin daji wirin Ɗan ƙarami. Daga baya sai suka aika wa hakimin da sako cewa lallai ya tabbata an dawo masa da mashinan.
” Ko da suka isa gidan ba su tafi da kowa ba sai shi hakimin. Ya bi su salin alin saboda kada ayi kashekashe a gidan
Bayan haka wasu maharan daban sun afka rukunin gidaje na Damba dake Gusau sun sace wani ma’aikaci da wasu ɗalibai da wasu mutane biyu.
Majiya ta shaida cewa kwatas ɗin Damba zama shifa da alwalanka ganin yadda ƴan bindigan ga suka surfafi gidajen babu ƙaƙautawa.
Abin ya yi matukar muni.
Discussion about this post