Ministan albarkatun ruwa Hassan Adamu ya bayyana cewa jihar jigawa ta cika dukkan sharuɗɗan sallama da yin bahaya a filin Allah Ta’ala.
Adama ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a shirin da ma’aikatar ke yi domin bikin ranar ɗakunan bahaya ta duniya da za ayi a watan Nuwamba.
” Jihar Jigawa ta buɗe wuta kuma ta cancanci yabo ganin ta iya kawo ƙarshen wannan matsala har an bata lambar yabo daga hukumar duniya.
A cewarsa, taron da Najeriya zata ƙarɓi bakunci, wani dandali ne na masu ruwa da tsaki, inda za a tattauna inganta dabaru da magance kalubalen tsaftar muhalli a kasar nan.
“Za su samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin da ke tattare da bahaya a waje da kuma ƙarancin gidajen bahaya. Har ila yau, wata cikakkiyar dama ce ta zaburar da al’umma, masu ruwa da tsaki da kamfanoni masu zaman kansu wajen maida hankali akan wannan matsala.
Discussion about this post