Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed ta shaida wa kwamitin kuɗi na majalisar Dattawa cewa gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emiefile bai shawarce ta ba kafin ya yanke shawarar chanja kuɗin Kasa.
Ta ce ” A matsayina na babbar ma’aikaciya a ma’aikatar kuɗin kasa kuma masaniya a harkar tattalin arzikin kasa amma kuma ace wai za a yi abu irin haka ba a shawarce ni ba.
” Ga shi kuma tun daga sanar da maganar sauya fasalin kuɗin dala sai kara lulawa ya ke yi. Cikin kwanaki kaɗan yanzu dala ya kai kusan naira 800. Idan ba a maida hankali ba zai kai har sama da naira 1000.
Mutane na gaggawar canja kuɗaɗen su zuwa kuɗaden waje musamman dala saboda gudun kada su rasa kuɗaɗen. Shi ya sa dala yanzu ya yi tashin gwauron zabi.
” Ni fa a ganina an yi gaggawar sauya fasalin kuɗi, ba yanzu ya kamata a yi hakan ba. Wannan lokaci da aka zaɓa bai da ce ba, kuma za a samu matsala idan ba a yi takatsantsan ba.
Tsohon mataimakin gwamnan CNN, Kinsley Moghalu ya ce tabbas a wanna lokaci da aka shirya sauya fasalin kuɗin za a iya samun miskila, domin wasu za su rika ƙin karbar tsoffin kuɗin lokacin da wa’adin da gwamnati ya cika.
Hakan zai kawo matsalar gaske wajen cinikayya da kasuwanci, amma kuma tsarin abu ne mai kyau da zai gyara yadda kuɗi ke musayar hannu a kasar nan.
Shi kansa bankin duniya ya shawarci Najeriya ta bi a hankali wajen sabon tsarin
Discussion about this post