Babban Manajan Kamfanin NPMS, reshe daga kamfanin fetur na ƙasa, NNPCL, Bala Wunti, ya ce a duk wata ana satar ɗanyen mai aƙalla ganga 470,000 a ƙasar nan.
Wunti ya yi wannan bayani lokacin da ya ke rangadin duba kadarorin NNPCL.
Ya ce an ƙiyasta ɗanyen man da ake dacewa ɗin duk wata zai kai na dala miliyan 700.
Sannan ya ce rabon da bututun mai na Bonny Terminal ya Yi aiki tun cikin watan Maris, saboda ɓarayin ɗanyen mai masu fasa bututu.
Ya ce wannan matsala ta haifar wa Najeriya ƙarancin kuɗaɗen shiga, kawo cikas wajen raba man gas da kuma haifar da ƙarancin ɗanyen man da ake haƙowa.
Haka a ƙarshen watan Agusta shi ma Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce da haɗin-bakin mutanen yanki, shugabannin addinai da jami’an tsaro ake satar ɗanyen mai.
Shugaban Kamfanin mai na NNPCL Mele Kyari ya yi ƙorafin yadda ake ɗirka gagarimar satar ɗanyen mai a Najeriya.
Da ya ke jawabi lokacin taron tattaunawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Tarayya a ranar Talata, Kyari ya ce kashi 95 bisa 100 na ɗanyen man da ake haƙowa a tashar Bonney duk ɓarayin da ke fasa bututu ne ke sace shi.
Daga nan kuma ya koka kan yawaitar wuraren da ake tace ɗanyen man da ɓarayin ke sata a cikin daji.
Kyari ya ce akwai hannun shugabannin coci-coci da na wasu malaman da ke kula da masallatai har ma da jami’an tsaro wajen satar mai ta hanyar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai.
Ya ce a ƙoƙarin hana satar ɗanyen mai, NNPC ta haɗa kai da jami’an tsaro ta lalata tankuna 959 waɗanda ɓarayin mai ke tara man da su ka sata.
An kuma lalata takunan ƙasa 737, ramun ɓoye mai a ƙasa guda 452, tukanen tafa abinci 355, kwale-kwalen katako wanda ake jidar ɗanyen mai da su guda 179.
Ya ce an samu wannan gagarimar nasara daga watan Afrilu zuwa Agusta na wannan shekara.
Kyari ya ce jami’an tsaro sun ƙwato kayayyaki daban-daban da ake amfani da su wajen fasa bututu da kuma satar ɗanyen mai.
Haka nan kuma ya ce an ƙwace jiragen ruwan satar ɗanyen mai guda 11, ƙananan kwale-kwale masu gudun tsiya guda 30, tamkar ɗaukar mai 30, kuma an damƙe mutum 122 da ake zargi da satar ɗanyen mai cikin waɗannan watanni biyar.
“Ana gagarimar satar ɗanyen mai daga bututu tun daga Atlas Cove har zuwa Ibadan da ma sauran daffo ɗin mu 37 a faɗin ƙasar nan.
“Dalili kenan a yanzu ba mu iya aika mai ta bututu. Wasu bututun ma an kai shekaru 15 ba su yi aiki ba.
“Satar mai kuma kowa na ciki, kama daga mutanen yankuna, shugabannin addini da jami’an tsaro. Saboda babu yadda za a yi ka kawo manyan tirelolin ɗaukar mai a cikin yankuna masu jama’a da yawa, a riƙa lodi ana jigila ba tare da kowa ya sani ba.
“NNPC ta ƙwato lita miliyan 35.8 ta ɗanyen mai daga hannun ɓarayin mai, an kuma ƙwato lita miliyan 22 ta dizel. An ƙwato fetur kuma har da kananzir.”
Wani rahoto kuma ya nuna cewa yanzu ba Najeriya ce ƙasar da ta fi yawan haƙo ɗanyen mai a Afrika ba.
Angola ta shige gaban Najeriya a matsayin ƙasar da ta fi sauran ƙasashen Afrika haƙo ɗanyen mai a kullum, inda a yanzu Angola na haƙo ganga miliyan 1.17 a kullum, Najeriya kuma ganga miliyan 1.13 a kullum.
Tsawon Shekaru 10 Najeriya ta shafe na ta matsayin ta farko wajen haƙo ɗanyen mai mai yawa a kullum, amma a cikin 2017 Angola ɗin dai ta taɓa shiga gaban Najeriya.
Satar Ɗanyen Mai: Haɗin Baki Tsakanin Ɓarayin Cikin Ofis Da Ɓarayin Cikin Daji:
Satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta ta zama wata gagarimar hanyar satar dukiyar gwamnati, kuma hanyar da wasu ke samun mahaukatan kuɗaɗe.
Masu satar ɗanyen man su na da alaƙa da ‘yan siyasa, manyan jami’an gwamnati kai har ma a cikin sojoji.
Haka kuma yayin da wannan gagarimar satar ɗanyen mai da ake yi a yankin Neja Delta, ya na da barazanar lalata muhallin yankin.
Rigingimun yankin sun haifar wa Najeriya asarar dala biliyan 1 daga Janairu zuwa Maris, wato watanni uku kenan. Kuma ɓarayin ɗanyen mai ne ke ci gaba da satar kuɗaɗen.
Dala biliyan 1 kuma ta yi daidai da adadin kuɗaɗen da ake buƙata wajen samar wa mutum miliyan 4.1 abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabas ɗin ƙasar nan, kamar yadda Majisar Dinkin Duniya (UN) ta yi hasashe.
Idan aka ci gaba da haka a Najeriya, to Libiya ma wadda a halin da ake ciki yanzu ta na iya haƙo ganga miliyan 1.08, alamomi na nuna cewa idan Najeriya ta ci gaba a haka, to Libiya za ta doke ta.
Cikin Agusta Najeriya ta haƙo ganga 972, 200.
Wannan yawan satar ɗanyen mai kuwa ta janyo Najeriya ba ta amfana da tsadar da fetur ya yi a lokacin yanzu na yaƙin Rasha da Ukraniya.
Sauran dalilan sun haɗa da yawan kuɗin tallafin fetur da Najeriya ke yi.
Najeriya dai ta ce ta na sa ran kashe Naira tiriliyan 6.7 wajen biyan tallafin fetur a 2023.
Discussion about this post