Shugaban hukumar kula da muhalli na jihar Bauchi BASEPA Ibrahim Kabir ya bayyana cewa ambaliyar ruwan sama ya rusa gidaje 1,453 sannan mutum 3 daga kananan hukumomin Zaki da Gamawa sun rasu.
Kabir ya fadi haka ne da yake sanar wa gwamnan jihar Bala Mohammed ibtila’in da ya samu mutane a wadannan kananan hukumomi a ranar da gwamnan ya kai wa karamar hukumar Zaki ziyara.
Kabir ya ce ambaliyar ya rusa gadan dake hada kauyukan dake kananan hukumomi biyu da wasu garuruwa a jihar.
” Wadannan mutane na bukatar kwalekwale 14 da za su rika amfani da su domin ci gaba da harkokin su.
Ya yi kira ga waɗanda ambaliyar ya shafa da su gaggauta neman mafaka domin samun kariya.
A nashi jawabin sa gwamna Bala Mohammed ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalen da suka rasa ‘yan uwansu a ambaliyar.
Mohammed ya bayyana cewa kauyuka a jihar na cikin hadarin ambaliyar ruwan sama domin duk shekara jihar na asarar rayuka da dukiyoyi a dalilin ambaliyar ruwa.
Discussion about this post