Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wani matashi mai shekaru 26 Chisom Nweke dake amfani da tsafi yana damfarar masu kasuwanci POS a jihar.
Kakakin rundunar Tochukwu Ikenga ya sanar da haka a garin Awka a cikin akon jiya.
Ikenga ya ce rundunar ta kama Nweke dan asalin kauyen Umuawulu dake karamar hukumar Awka ta Kudu ranar Alhamis.
Ya ce Nweke ya bayyana wa ‘yan sanda cewa ya damfari wasu masu sana’ar POS dake Awka da kauyukan dake kusa da Awka.
Ikenga ya ce Nweke ya ce shi dan kungiyar ‘yan fashi da makami ne da suka shahara wajen yi wa mutane fashi.
” Nweke kan damfari masu POS ta hanyar ba mai POS takarda da ya riga ya yanka kamar kudi domin ya saka masa a cikin asusun sa na banki.
“Mai POS zai karbi wadannan takardu wanda a lokacin yake gani kudi ne sannan ya aika da anihin kudi zuwa asusun Nweke.
Damfarar masu POS
Masu sana’an POS sun koka kan yadda mutane ke damfaran sua sana’ar.
‘Yan sanda sun kama mutane da dama da laifin damfarar masu POS a kasar nan.
A watan Agusta 2021 ‘yan sanda sun kama wani a jihar Ondo da ya rika damfarar masu POS ta yanar gizo.
A Yuly 2020 jami’an tsaro sun kama wani da ya yi kokarin damfarar mai POS a kasuwar Oko dake Asaba jihar Delta.
Discussion about this post