Akalla jarirai 25 ne aka haifa a sansanin da aka kebe wa wadanda suka rasa matsugunan su dake kauyen Karnaya a karamar hukumar Dutse jihar Jigawa.
Karnaya kauye ne dake da nisan kilomita 23 daga Dutse babban birnin jihar kuma yana daga cikin kauyukan da ambaliyar ruwa ya ya wa ta’adi matuka.
Mazaunan kauyen sun ce ambaliyar ruwan ya rusa gidaje sama da 500 wanda mafi yawan su gidajen laka ne da dole mutanen dake kauyen suka nemi mafaka a kangon ginin gidajen mai da makarantu.
Wani shugaban al’umma dake zaune a sansanin mai suna Falalu Ado ya bayyana wa manema labarai ranar Laraba cewa gwamnati ta yi watsi da taimaka musu a sansanin.
Ado ya ce mata 25 ne suka haihu a sansanin ba tare da taimakon kwararrun ungozoma ba.
“Muna bukatar abinci da magunguna domin na ji labarin cewa cutar kwalara ta barke a sansanin.
“Mata na haihuwa ba tare da taimakon jami’an lafiya ba. Yanzu muka kammala radin sunan daya daga cikin jariran da aka haifa a sansanin mun rada masa sunan sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani saboda yadda ya rika tallafa mana da abinci a sansanin.
Ya ce sarkin Gumel da sarkin Dutse Nuhu Muhammad-Sanusi sun tallafa musu da kayan abinci tun da suka shigo sansanin.
Ado ya ce karamar hukumar Dutse ta bada gundumar buhunan garin kwaki biyar da buhun siga daya a lokacin da suka fara sauka a sansanin sannan hukumar bada agajin gaggawa na jihar ta bada gundumar buhunan garin kwaki 10.
Discussion about this post