‘Yan Sandan Ƙasa-da-ƙasa (Interpol) sun damƙe Tukur Mamu a filin jirgin saman Cairo na ƙasar Masar.
An kama Mamu a lokacin da ya ke jiran wani jirgi wanda zai shiga zuwa Saudi Arabiya daga Cairo, babban birnin ƙasar Masar.
Mamu wanda shi ne mawallafin jaridar Desert Herald, ya kasance mai sasantawa da shiga tsakanin ‘yan ta’adda ana sakin wasu fasinjojin da ‘yan ta’adda su ka kama tun cikin watan Maris, 2022.
Sai dai kuma ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan an kama shi, an taso ƙeyar sa zuwa gida Najeriya tare da matan sa biyu, da wani ɗan rakiya ɗaya da ba a bayyana kowane ba.
Zai fuskanci tambayoyi daga jami’an SSS bayan ya sauka filin jirgin saman Malam Aminu Kano ranar Laraba da rana.
Mamu dai a baya ya ce ya daina shiga tsakani ana sakin waɗanda aka yi garkuwa da su, tun bayan da ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na yi wa rayuwar sa barazana.
Har yanzu dai akwai sauran fasinjojin jirgin ƙasa a hannun ‘yan ta’addar da su ka yi garkuwa da sama da mutum 64 a lokacin.
Discussion about this post