Nan da wasu watanni, duk d’an siyasa mai kujera, tun daga majalisar jiha har ofis din shugaban kasa sai ya shiga zabe. Ko dai ya sake ci ko kuma a bugashi da kasa saboda gazawarsa ko guguwar canji. Zabe hisabin ‘yan siyasa ne na duniya. Halin kowa ne zai bishi.
A kowacce jamhuriya ta siyasa, ana iya samun guguwar siyasa. Ita ce take kwaso mutane iri iri su samu damar cin zabe. Idan Allah ya taimaki talakawa sai ta kwaso musu nagari. Tana iya zuwa da wasu bayin Allah wadanda mutane su ke so, kamar yadda take kwaso baragurbi da yawa wad’anda su ke shiga alfarmar jami’ya ko wani babban dan takara.
A shekarun baya, a zabuka da yawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa wasu yan siyasa rumfa sun ci zabe tun kafin ya zama shugaban kasa. Bayan an kafa APC ya kuma zama dan takararta na shugaban kasa, wanda farin jininsa a 2015 ya kunno guguwar canji a Najeriya. Ko yanzu akwai alamun wannan guguwar?
Kowacce jami’ya a tsakanin manyan jami’yyu da wasu jami’yyun na Najeriya ta fitar da dan takarar shugaban kasarta. Jami’yar APC mai mulki ta fitar da tsohon gwamnan Lagos, Bola Ahmad Tinubu. A yayin da PDP babbar jami’yar adawa ta fitar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya tsaya a sabuwar jami’yarsa, NNPP. A bangaren jami’yar LP kuma, akwai tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.
Gaskiya, babu bako a cikin yan takarar da su ke zawarcin shugabancin Najeriya. Kowannensu ya ta6a zama “His Excellency”. Alhaji Atiku Abubakar ma ya ta6a zama mutum na biyu a Najeriya. Halin kowa ne zai ceceshi. Yiwa mutumin da aka sani hisabi babu wahala akan wanda ba a sani ba. Dukkaninsu sanannu ne. Talakawa, za6i yana hannunku.
Allah ya kaimu zabe cikin aminci.
Discussion about this post