Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta bayyana cewa ta na goyon bayan matsayar ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, wanda ya ce bai yarda Najeriya ta cire tallafin fetur ba, har sai ranar da aka fara tace ɗanyen mai a cikin Najeriya, aka daina shigo da shi daga waje tukunna.
Shugaban NLC Ayuba Wabba ya Yi wannan sanarwa kuma ya sa mata hannu aka raba wa manema labarai a ranar Asabar, a Abuja.
Jawabin NLC ya fito ne sakamako ƙalubalantar da Kakakin Kamfen ɗin Takarar Tinubu 2023, Festus Keyamo, wanda ya ce ya na jiran ya ji ra’ayin su kan kalaman da Peter Obi ya yi cewa zai cire tallafin fetur idan ya zama shugaban ƙasa.
Wabba ya ce NLC za ta fito da daftarin da ma’aikata za su ƙayyade wa ‘yan siyasa buƙatun su domin tunkarar su da buƙatun tun kafin a kafa wata sabuwar gwamnati.
“Ɗaya daga cikin buƙatun mu shi ne tilas a fara gyara matatun mai a mu tukunna.
“Kuma tilas za mu nemi a daina shigo da fetur ɗungurugum daga ƙasashen ƙetare.
“Tun shekaru da dama a baya NLC ta sha cewa hanya daya da za a bi don a daina bayar da tallafin fetur, ita ce a gyara matatun mai na cikin gida.
“Ya kamata a yi amfani da hankali a nan, babu wata fa’ida a riƙa sayo fetur da tsada daga ƙasashen wajen, fetur ɗin da mu ke da halin iya tace shi nan a cikin Najeriya ” Cewar NLC.
“Idan ana so tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa, idan ana so tattalin arzikin mu ya tashi daga ‘yan cima-zaune mu koma masu fitar da kayan sayarwa masu albarka a duniya, to sai an cire talalfin fetur, wanda cire shi kuwa ba zai iya yiwuwa ba, har sai an gyara matatun mai na ƙasar nan tukunna.” Inji shi.
Discussion about this post