Bayanan abin da aka tattauna a taron da Gwamna Nyesom Wike ya yi da makusantan sa, kuma jiga-jigan PDP waɗanda yawancin su gwamnonin PDP ne da ke goyon bayan sa sun fito fili.
A ranar Lahadi ce Wike ya karɓi baƙuncin su a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas, a Maitama, Abuja.
Yawancin waɗanda su ka halarci taron duk gwamnonin da su ka goyi bayan sa ne a zaɓen fidda-gwani, wanda Atiku Abubakar ya yi nasara a kan sa, shi kuma ya zo na biyu.
Da ya ke magana bayan kammala taron, Jerry Gana, wanda mamba ne a Kwamitin Amintattun PDP, ya shaida wa manema labarai cewa gungun magoya bayan Wike sun yi taro ne a karon farko tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, domin su yi bitar abin da ya faru da yadda zaɓen ya kasance, sai kuma matsayin da PDP ta ke a yanzu lokacin da zaɓe ke gabatowa.
Gana ya ce sun ɗauki wata matsaya, amma bai faɗi ko guda nawa ba ne, kuma bai ambaci ko da guda ɗaya ba.
“Mun san dai abubuwa za su kasance, to idan sun kasance ɗin, za mu yi wa ‘yan Najeriya bayani. Saboda wannan ne haɗuwar mu ta farko, tun bayan zaɓen fidda-gwanin da PDP ta gudanar.
“Mun fito ƙarara a tsakanin mu, mun yi bitar batutuwan da ke gaban mu. Kuma mu na sanar da ku cewa kan mu a haɗe haɗe ya ke, a matsayin mu na magoya bayan Wike.”
Majiya a cikin waɗanda su ka halarci taron ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an tattauna tsawon lokaci kan sa-toka-sa-katsin da ake yi tsakanin Wike da Atiku Abubakar.
Wike ya ƙi yarda ya zauna da Atiku tun bayan da ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta matsayin mataimakin takarar sa.
A ranar Juma’a ce Wike ya yi wa Atiku raddin cewa maƙaryaci ne. Kuma wannan rikici ne aka ce ya kawo wa Atiku tsaikon kafa kwamitin kamfen na yaƙin neman zaɓen sa.
Majiya ta ce gungun ‘Wikekeniya’ sun nemi lallai sai dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka, ta yadda wani daga kudu zai zama shugaban jam’iyya.
Sun ce wannan ɗaya ne daga cikin sharuɗɗan da su ka gindaya kafin su taka rawa a kamfen ɗin Atiku Abubakar kafin zaɓen 2022.
Gungun sun koka kan yadda shugabancin PDP ya koma kacokan a hannun ‘yan Arewa, alhali kuma daga Arewa ne ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito.
Yayin da shugaban PDP Ayu ɗan Jihar Benuwai ne, kuma na hannun damar Atiku, shi kuma Atiku ɗan Jihar Adanawa ne, duk daga Arewa.
Haka nan kuma sun ce Mataimakin Ayu, Umaru Damagun ɗan Arewa ne daga Jihar Yobe. Haka shi ma Shugaban Kwamitin Amintattun PDP, Walid Jibrin ɗan Arewa ne. Sai Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP Aminu Tambuwal na Sokoto shi ma ɗan Arewa ne.
“Shin ta yaya jam’iyyar da ke tafiya falan-ɗaya za ta iya neman ƙuri’un ‘yan kudu?” Haka wata majiya ta bayyana.
Sun kuma zargi Atiku da yin saniyar-ware da sauran jiga-jigan jam’iyya waɗanda ba makusantan sa ba.
Sun zargi cewa har ma makusantan Atiku sun raba manyan muƙaman gwamnati a tsakanin su, tun ma kafin zaɓen 2023 ɗin ya zo, ba a ma kai ga cin narasa ba.
“Ta yaya ɗan takarar da ke haka tun a yanzu za a yi tsammanin zai canja idan ya zama shugaban ƙasa kuma?”
Aƙalla mutum 51 ne su ka halarci taron, ciki har da gwamnoni biyar, tsoffin gwamnonin PDP bakwai.
Akwai Suleiman Nazifi da tsohon Antoni Janar Mohammed Adoke. Sai Hosea Agboola, Phillip Aduda, Zainab Kure, Garba Lado, Sunday Onoh da sauran su.
Akwai kuma Mohammed Abacha da sauran su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Wike ya karɓi baƙuncin Gwamnonin PDP na yanzu da na da can.
Yayin da rashin jituwa tsakanin Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ke ƙara haifar da ɓaraka tsakanin sa da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, Gwamnonin PDP sun kai masa ziyara a ranar Lahadi.
Gwamnonin sun kai ziyarar ce kwana ɗaya bayan da manyan ‘yan tawayen APC, Yakubu Dogara da Babachir Lawal sun kai masa ziyara, jim kaɗan bayan dawowar sa daga bulaguro a ƙasar waje.
Gwamnonin da su ka kai wa Wike ziyara, sun je ne tare da wasu tsoffin gwamnonin PDP, inda a ranar Lahadi su ka gana da shi a asirce, a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ke Asokoro, Abuja.
Ba a san dai abin da su ka tattauna ba. Amma kuma tabbas tattaunawar ba ta rasa nasaba da saɓanin da ke ƙara tsanani tsakanin Wike da Atiku Abubakar.
An samu saɓani tsakanin manyan jiga-jigan PDP ɗin biyu, tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, inda Atiku ya yi nasara, shi kuma Wike ya zo na biyu.
Tun bayan kammala zaɓen dai Wike ya yi tsinuwa da Allah–wadai ga wasu manyan jam’iyyar da ya ce sun yi masa butulci, inda ake ganin da Gwamna Aminu Tambuwal ya ke, wanda ya janye kafin zaɓe, ya ce a zaɓi Atiku.
Wike ya kuma ragargaji masu zaɓen ‘yan takara daga Kudu, waɗanda ya ce sun sayar da ‘yancin ‘yan kudu saboda ‘yan kuɗi kaɗan.
Sannan kuma Wike ya ragargaji ɗaukar Gwamna Okowa na Jihar Delta matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku.
Daga baya Wike ya ce Atiku ya yaudare shi, domin bayan kammala zaɓe, ya bi Wike ɗin har gida ya ba shi haƙuri. Kuma ya ce shi zai ɗauka mataiakin takara.
Ɗaukar Okowa ya fusata Wike, inda ya riƙa fesa wa Atiku munanan kalamai, kuma har yau bai taya Okowa murnar zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP ba.
Kwanan nan Atiku ya fito ya ce masu ba shi shawarar wanda zai ɗauka mataimakin takara, ba su ba shi sunan Wike ba. Wannan furuci daga Atiku ya harzuƙa Wike, har ya kira Atiku ƙasurgumin maƙaryaci.
Gwamnonin da su ka ziyarci Wike sun haɗa da: Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Benuwai, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Okezie Ikpeazu na Abiya.
Tsoffin gwamnonin sun haɗa da Donald Duke na Cross River, Gabriel Suswan na Benuwai, Olusegun Mimiko na Ondo, Ibrahim Idris na Kogi da Johan Jang na Filato.
Jiga-jigan PDP sun fara ɗar-ɗar da Wike tun bayan da gwamnonin APC uku daga Kudu maso Yamma su ka kai masa ziyara. Sai kuma ziyarar da Yakubu Dogara da Babachir Lawal su ka kai masa a ranar Asabar.
An ruwaito Wike dai na cewa ba zai fita daga PDP ba.
Discussion about this post