Kakakin Kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Dele Alake ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Bola Tinubu ya isa ace ya shiga cikin jerin ‘yan mazan jiya irin su Awolowo, Sardauna da Azikwe.
Alake, ya ce ” Mutane a yanzu sun bata suna da kirarin da ake yi wa jarumai, Uwayen al’umma, Wato ‘GodFather’ suna rada wa kowani irin mutum, har da irin wadanda basu cancanta ba.
” Tinubu ya goya mutane, ya kafa mutane da har sun zama shugabanni a kasar nan. Wannan shine irin abubuwan da su Sardauna, Awolowo da Azikwe suka yi, da shima dole a saka shi a cikin jerin mutane irin haka.
Bayan haka Alake ya yi karin bayani game da hana tsohon gwamnan jihar Akinwumi Ambode sake takarar gwamna a jihar.
” Ambode ya kauce hanya. Ya zabi wata hanyar da ba ita ce tsarin jihar Legas ba. Dalilin da ya sa kenan gaggan ‘yan siyasa a jihar suka yi masa katanga da takarar gwaman jihar.
Discussion about this post