Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ya na kan shan caccaka bayan ya kira jami’o’in jihohi da su ka koma yajin aiki cewa duk “tubalin toka” ne.
Emmanual Osodeke ya kira su tubalin toka saboda sun amince su janye yajin aikin da ake kan yi a yanzu.
Ya yi furucin ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, dangane da irin tasirin da tsarin da gwamnatin tarayya ta ce za ta bi, wato ba za ta biya albashi ga duk wanda ya tafi yajin aiki ba. Gwamnati ta ce wanda ya je aiki kaɗai za ta biya albashi.
An tambaye shi wannan dalilin ne ya sa wasu jami’o’i janyewa daga yajin aiki, domin a riƙa biyan su albashi.
Daga nan sai Farfesa Osodeke ya ce dukkan jami’o’in da su ka janye daga yajin aiki, ba su cikin ƙungiyar ASUU.
“Idan ka na bayar da bayanin ƙididdiga ka riƙa duba tun can asali. Jami’ar Jihar Kwara ba ta cikin ƙungiyar ASUU. Jami’ar Jihar Osun kuwa an dakatar da ita daga ƙungiya saboda mugun halayen su. Ka je ka bincika ka gani. Jami’ar Jihar Legas (LASU) kuma mu na kotu da su saboda shekaru biyar baya an korar mana dukkan shugabannin ASUU na can. Ka ga ba su cikin wannan gwagwarmayar da mu ke yi yanzu kenan.
“Amma Jami’ar Ekiti da Gimbe, Yobe da ta Kaduna duk malaman su na da ‘yancin janyewa.
“Saboda haka kada ka kawo misalan waɗannan, domin ba su da wata alaƙa da mu kenan ta wannan gwagwarmayar. Kuma ka duba mana. Shin Jami’ar Ibadan, Nsuka, ko ta Ahmadu Bello da Jami’ar Bayero su na yajin aiki ko ba su yi? Maiduguri fa da ta Lagos? Na fi so mu yi maganar jami’o’in kirki ba makarantun tubalin toka ba.”
Wannan kalami ya janyo masa ragargaza daga malaman jami’o’i da ɗaliban ilmi sosai a faɗin ƙasar nan da kuma jami’o’i.
Cikin waɗanda su ka maida masa zazzafan raddi har da Jami’ar Jihar Ekiti.
Discussion about this post