Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta bayyana cewa ba za ta janye yajin aiki ba, har sai Gwamnatin Tarayya ta biya buƙatun da ƙungiyar ta gindiya tukunna.
Saboda duk wani zumuɗin da ake yi ana ganin cewa za a kawo karshen yajin aikin a cikin wannan makon, zai tashi ta iska, domin Shugaban ASUU Emmanual Osodeke, ya ce babu wata alamar da ke nuna za a kawo ƙarshen yajin aikin.
Osodeke ya ce ba gaskiya ba ne da Gwamnatin Tarayya ke kukan talauci, har ta ke cewa ba ta kuɗaɗen da za ta iya biyan buƙatun ASUU, domin a kawo ƙarshen yajin aikin.
Shugaban ya yi wannan jajircewar ce a Zauren Tattaunawar PREMIUM TIMES na shafin ta a Tiwita.
Sauran waɗanda suka tattaunawa ɗin sun haɗa da Goyon Falola da Daraktan Connect Hub NG, Rinu Oduala.
“Taron neman sasantawa tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya bai tsinana komai ba. Saboda babu wani abu sabo da gwamnati ta bijiro da shi a kan teburin tattaunawa.”
“Kwamitin Nimi Briggs bai zo da komai ba. Kawai da bayanin Hukumar Tantance Albashi da Ladar Biyan Ƙwadago ta Ƙasa su ka zo da shi.” Inji Shugaban ASUU.
Ya ce ‘yan Najeriya su shirya a zaɓen 2023 kada su zaɓi kowa sai waɗanda ke da kishin bayar da fifiko wajen bunƙasa ilmi da kula da jami’o’in gwamnati.
“Duk wanda a cikin masu kamfen a yanzu ya kasa gabatar ma ku da daftarin yadda zai inganta fannin ilmi, to kada ma a zaɓe shi.”
Daga cikin buƙatun da ya ce ASUU na so a cika masu kafin su janye yajin aiki, akwai yin amfani da tsarin biyan albashi na UTAS, Gwamnatin Tarayya ta amince da yarjejeniyar 2009, a dakatar da yawan kafa jami’o’i barkatai, a sakar wa jami’o’i kuɗaɗen farfaɗo da darajar ilmi da sauran su.
Ya ce idan ba a biya masu waɗannan buƙatun ba, to ba za su janye yajin aiki ba.
Discussion about this post