Gwamnonin Najeriya sun ragargaji Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, bayan ya sake yin iƙirarin cewa gwamnonin ba su da damar cewa ba za su biya ‘yan ‘gada-gada’ kuɗaɗen su dala miliyan 418 ba.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya ragargaji Malami bayan wata ganawa da Gwamnonin su ka yi ranar Laraba a babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa.
Fayemi ya yi ragargazar tare da zargin cewa Malami ya haƙiƙice a biya kuɗaɗen don wani ra’ayi na sa kaɗai, amma ba don bin abin da dokar ƙasa ta tanadar ba.
Gwamnan na Ekiti ya bayyana cewa, “Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta sake nazarin yunƙurin da Ministan Shari’a Abubakar Malami yi, inda ya nemi ya tsallake matakan doka da yin fatali da hukuncin Kotun Ƙoli. Ya nemi iznin Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannun amincewa a fara cirar kuɗaɗen Paris Club ba bisa ƙa’ida ba.
“NGF mun kafa kwamitin da ya ƙunshi Shugaba kuma Gwamnan Ekiti, Gwamnan Ondo, na Filato, Nasarawa da Ebonyi cewa su zauna tare da Kwamitin Shugaban Ƙasa su tattauna lamarin.
“Amma dai mu Gwamnonin Najeriya mi na nan kan matsayin mu cewa babu wanda zai fara cirar kuɗaɗen saboda magana ta na kotu, kuma Kotun Ƙoli ta bada umarnin kada a fara cirar kuɗaɗen.
“To amma abin na damun mu ganin yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ke ta bi kafafen yaɗa labarai ya na kamfen ya na nuna cewa lallai sai a fara cirar kuɗaɗen, saboda wai mu ne muka ci ladar kuturu, kuma mu ka amince za mu yi masa aski. Amma ba haka ba ne.”
Gwamna Fayemi ya ce ba su amince da kalaman da Malami ya riƙa kafa hujja da su ba.
Ya ƙara da cewa gaba ɗaya batun cewa an yi aikin da ya cancanta mu gwamnoni mu biya bashin, ba gaskiya ba ce, damfara ce, gidoga ce, kuma gada-gada ce kawai.”
Kuɗaɗen da ake neman a biya ɗin dai an yi ikirarin an yi ayyukan a ƙananan hukumomi 774, tun shekaru masu yawa da su ka gabata, kafin waɗannan gwamnonin su hau mulki.
Amma Gwamna Fayemi na Jihar Ekiti bai amince ba, ya ƙi karɓar tayin da su ka yi masa, inda ya tsaya kai da fata cewa lallai sai dai a yi ƙwaƙƙwaran binciken ƙwaƙwaf domin a gano gaskyar lamarin.
Sai dai kuma bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa wannan ƙaƙudubar, an riƙa ɗaukar nauyin buga wasu bayanan ɓata suna ga Gwamna Fayemi a cikin kafafen yaɗa labarai.
Cewa aka riƙa yi wai Fayemi an ƙi amincewa da roƙon da ya yi na a datse kashi 10 cikin 100 na bashin.
Salsalar Wannan Hukuncin Biyan Bashi:
Batun wannan bashi da ake tankiya da tababar sa, ya samo asali ne daga wani hukuncin da kotu ta yanke cewa wasu ’yan kwangila da jami’an tuntuɓa na bin jihohi da ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan basussuka.
Wasu ’yan gidoga su ka yi iƙirarin cewa su jami’an tuntuɓa ne su ka ce sun taimaka wa ƙananan hukumoni da jihohi domin su karɓo kuɗaɗen su da aka cira fiye da kima tsakanin 1995 da 2002 domin biyan bashin Paris Club.
Wasu ‘yan kwangila kuma daga cikin su wai sun yi wa ƙananan hukumomi 774 ayyuka bashi, saboda zaman jiran tsammanin za a biya kuɗaɗen Paris Club a biya su daga ciki.
A baya PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomin Najeriya, ALGON ya nuna goyon bayan a biya kuɗaɗen.
Buhari Ya Sani Ya Yi Shiru:
PREMMIUM TIMES ta buga labari a cikin Janairu, yadda Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara tare da sanar da shi cewa cewa kada ya bari a biya kuɗaɗen, domin babu wata ƙwaƙƙwarar hujjar an yi ayyukan bashin.
Sai dai kuma duk da wannan gargaɗin Buhari bai taka wa su Malami burki ba
Sai ma da ta kai ga Malami ya samu saƙonnin gargaɗi daga wurare uku, ciki har da EFCC su na shaida masa cewa kada ya shiga gaba a biya bashin, domin akwai gidoga a cikin lamarin.
Cikin waɗanda su ka gargaɗi Minista Malami har da Shugaban ALGON na baya-baya, wanda shi ma ya nuna cewa kamfanonin tuntubar masu cewa su ne dillalan waɗanda ke bi bashi, ba su san da zaman su ba.
Yayin da su Malami su ka matsa lamba har Buhari ya sa hannu kan cakin kuɗin alƙawarin biya (promisory note), a ranar 4 Ga Disamba, 2020, su ma Gwamnomin daga baya cikin Janairu sun samo wani sabon umarni daga Buhari cewa kada a biya kuɗaɗen, har sai an yi ƙwaƙƙwaran bincike. Amma yanzu kuma Buhari ya amince a biya kuɗaɗen, ba tare da ya koma ta kan shawarar da Gwamnonin Najeriya su ka ba shi ba.
Agusta 2022:
Buhari ya dakatar da Malami da Ministar Kuɗaɗe daga fara cirar kuɗaɗen jihohi, domin fara biyan ‘yan gidoga.
Discussion about this post