Gagarimar satar jidar biliyoyin dalolin Najeriya da iyalan Abacha su ka riƙa yi a zamanin mulkin sa, sai kuma farautar nemo kuɗaɗen da aka riƙa yi bayan mutuwar sa, ta kasance ɗaya daga cikin labarin mashahuriyar satar kuɗaɗe daga wata ƙasa ana ɓoyewa wasu ƙasashe a tarihin duniya.
1. Harƙallar Satar Kuɗi Da Sunan Inganta Tsaro:
Tsakanin 1994 zuwa 1998, Sani Abacha da Mashawarcin Harkokin Tsaron sa Ismaila Gwarzo sun rubuta bayanan tsaro na ƙarya har sau 60, domin su riƙa kwasar maƙudan kuɗaɗen da su ka kai dala biliyan 2 lakadan daga CBN, a lokacin bankin na ƙarƙashin Paul Ogumah.
Maimakon a riƙa yin ayyukan inganta tsaro da kuɗaɗen, sai aka riƙa lodi da jigilar su zuwa asusun makusantan Abacha a ƙasashen waje, kamar su ɗan sa Mohammed Abacha da Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi na yanzu.
2. Ƙarfin Hali Ɓarawo Da Amsa Marhabin:
Yadda Mohammed Abacha Da Atiku Bagudu Su Ka Nemi Bai Wa Najeriya Bashin Biliyoyin Dalolin Da Su Ka Sata Daga Najeriya:
Waɗannan tantiran ‘yan gadangarƙama su biyu, sun yi wani yunƙurin rainin wayau, wanda su ka nemi bai wa Najeriya ramcen maƙudan kuɗaɗen da su ka sata su ka ɓoye a waje. Ba tsoro babu fargaba, haka su ka nemi su dawo da kuɗaɗen a matsayin lamuni ga Najeriya, tare da ɗora kuɗin-riba masu tarin yawa.
4. Bashin Bai Wa Ɓarayi Lasisin Ci Gaba Da Ɗirka Harƙalla:
Wannan wani tsarin iya-shege ne kuma da su ka damfari Najeriya dala miliyan 282 ta hanyar yi wa Gwamnatin Najeriya ingiza-mai-kantu-ruwa, ta sayi wani bashi da Najeriya ke bin kamfanonin su. Inda abin ya fi ciwo, An sayi bashin ne nunkin kuɗin da ya kamata a ce sun cancanci farashin bashin.
4. Rashawa: Yadda aka riƙa tatsar kuɗaɗen rashawa da cin hanci daga kamfanonin da su ka riƙa yi wa gwamnati kwangiloli a lokacin, irin su kamfanin Dumez na ƙasar Faransa.
Bincike Daga Cikin: Pandora Papers, Ma’aikatar Shar’a ta Amurka (USDJ), Africa Confidential da Bayanan Kotun Switzerland.
Discussion about this post