Akalla mutum 51 ne ‘ya bindiga suka kashe daga ranar 26 ga Yuni zuwa daya ga Yuli a kasar nan.
Bisa ga rahotannin da gidajen jaridu suka wallafa wanda PREMIUM TIMES ta samu ya nuna cewa mafi yawan mutanen da ‘yan bindigan suka kashe jami’an tsaro ne.
Daga cikin mutum 51 din da aka kashe mutum 40 jami’an tsaro ne inda a ciki mutum 10 ‘yan sanda ne sai kuma sojoji 30.
Sauran mutum 11 din farin hula ne.
Daga ckin mutum 51 din da aka kashe ‘yan bindiga sun kashe mutum 43 a karamar hukumar Shiroro jihar Neja.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan sannan ya tabbatar cewa gwamnati za ta dauki mataki domin hukunta ‘yan bindigan da suka aikata haka.
Edo
‘Yan bindiga sun kashe faston cocin Katolika dake Auchi a jihar Edo Christopher Odia.
Maharan sun kashe limamin bayan sun yi garkuwa da shi ranar Lahadin makon jiya.
Odia ya rasu yana da shekaru 41 inda kafin ya rasu shine shugaban fastocin cocin Katolika na St Michael dake Ikabigbo a karamar hukumar Etsako sannan shugaban makarantar sakandare na St Philip dake Jattu.
Rivers
‘Yan bindiga sun kashe wani sufritandan ‘yan sanda a karamar hukumar Oyigbo dake jihar Rivers.
Dan sandan ya gamu da ajalinsa a Oyigbo yayin da yake hanyar dawowa daga wurin aiki ranar Laraban da ya gabata.
Ebonyi
A ranar Litini din makon jiya ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a harin da aka yi a kauyen Ngbo dake karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi.
Maharan sun lalata kayan da ya kai miliyoyin kudi a jihar.
Enugu
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a shingen tsaron da ‘yan sanda suka kafa a hanyar Agbani dake karamar hukumar Enugu ta Kudu dake jihar Enugu.
Maharan sun kashe jami’an tsaro ranar Alhamis din da ya gabata da misalin karfe 9 na safe.
‘Yan bindigan sun kashe jami’an tsaron ne a lokacin da suka buda musu wuta a shingen tsaron.
Neja
‘Yan bindiga sun kashe mutum 43 inda a ciki akwai sojoji 30 da ‘yan sanda mobal 7 a harin da suka kai a wurin hako ma’adanai dake karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Maharan sun kashe wadannan mutane ranar Laraban da ta gabata a kauyen Ajata- Aboki.
Kaduna
‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro da farin hula a kauyen Sabon Gero Wanda aka fi sani da ‘New Millennium City’ dake karamar hukumar Chikun ranar Talata.
A wannan rana maharan sun yi garkuwa da mutum 16 daga wannan gari.
Discussion about this post