Tsohon gwamnan jihar Legas, kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya karyata labaran da kakafen yaɗa labarai ruka buga cewa wai ya caccaki shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A wata doguwar sanarwa wanda ya fitar ranar Juma’a, Tinubu ya ce ƴan jarida ne suka lauye maganar domin kawai su samu abin yaɗa wa duniya amma abinda ya faɗi ba abinda aka ruwaito bane.
” Ni ban faɗi duk abinda ake cewa ma faɗi game da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba. Gaggawar a rubuta labari ne yasa wasu suka lauya kalamai na suka yi masa munanan fassara domin su ɓata ni.
” Na yi magana da yarbanci ne, dalilin haka yasa ƴan jarida kowa ya riƙa kantara irin nashi fassarar, da abin da na ce da abinda ban ce ko ya lafta a jaridar sa. Amma ba zai yi ƙaranta ba in soki ofishin da nake nema nima in shiga. Yin kaha ƙaranta ne kuma na fi karfin yin haka.
” Shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai dattaku da sanin ya kamata, mai kuma kaunar talakawa. Dalilin haka ne ya sa dimbin talakawan Najeriya ke kaunar sa suka kuma mara masa baya.
” Ina mai farincikin zama ɗaya daga cikin waɗanda suka haɗa hannu kuma ke kangaba wajen gwagwarmayar kafa jam’iyyar APC.
Hakika, na ci gaba da goyon bayan shugaban kasa da gwamnatinsa. Ko da a lokacin da gwamnati ta sha suka sosai, ina tare da shugaban kasa kud da kud sannan da kansa Buhari ya zabe in shugabanci kamfen dinsa a 2019.