Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin da ya tantance ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ƙaryata rahoton cewa wai jam’iyyar APC ta dakatar da wasu mutum 10 daga takarar shugaban kasa.
Wannan mamba wanda baya so a bayyana sunan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu maganar dakatar da wasu ƴan takara daga fafatawa a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar za ta gudanar a farkon makon gobe.
Majiyar mu ya shaida mana cewa abinda suka yi shine ” A lokacin da muka kammala tantance duka ƴan takara sai muka samu wasu daga ciki su 10 da basu da ƙarfin iya fafatawa a zaɓe da jam’iyyar Adawa a babban zaɓe dake tafe.
” Dalilin haka sai muka shawarce su da su janye su mara wa wasu daga cikin ƴan takara 13 da ake ganin suna karfi a siyasance.
” Babu wanda a ka cire ko dakatar daga cikin duka ƴan takara 23 da aka tantance. Shawara ce muka baiwa wasu mutum 10 daga cikin su saboda basu da karfin iya cin zaɓe a siyasance sai muka basu shawarar su janye. Hakan ma ba dole bane.
” Idan mutum ya ga dama ya janye toh, idan bai ga ga zai iya hakan ba, babu tilas ya cigaba da takarsa a je a fafata a filin zaɓe.
A karshe ya ce mutane ne badu fahimci bayannan da shugaban kwamitin Oyegun ya yi ba saboda. Sun yi masa bahaguwar fassara.
Abinda ake so dai shine a samu haɗin kai domin kada a tafi zaɓe da yawan ƴan takara har 23.
Discussion about this post