Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya bayyana cewa babban abinda zai fi maida hankali a kai idan ya zama gwamnan Kaduna shine mafance matsalar tsaro a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya kaddamar da kwamitin Kamfen ɗin sa a garin Kaduna, Ashiru ya ce dalilin matsalar rashi tsaro da rarrabuwar kai a jihar Kaduna ya sa an samu koma baya a wajen cigaba da raya jihar
” Ina da kwarewa a harkar sanin yadda ake hulɗa da jama’a da kuma dabarun samar da zaman lafiya a tsakanin mutane. Idan na zama gwamna abinda zan fi maida hankali akai kenan. Haɗa kan ƴan jihar mu da kuma kawo cigaba masu ma’ana.
” Jihar Kaduna ta shiga ruɗu, ruɗun da ba za mu zuba ido mu bari shikenan ta nutse cikin baharmaliya ta halaka ba. Dole mu fantsama mu ceto ta tunda wuri. Wannan shine dalilin da ya sa na ke kokarin ganin mun haɗa kai na zama gwamnan jihar.
Ashiru ya kara da cewa gidan gwamnatin Kaduna kamar na shiga ne InshAllahu.
A karshe Honarabul Ashiru ya godewa kwamitin kamfen ɗinsa wanda ya ƙaddamar, yana mai cewa ” na kafa kwamiti ne da ya haɗa da dattawa da matasa waɗanda za su rika tallata manufar mu, su haɗo mana kan wakilan jam’iyyar mu sannan kuma jama’a domin samun nasara ga abinda muka saka a gaba.