Hukunar Zaɓe ta karyata raɗe-raɗin da kiraye-kiraye da ake ta yi a shafukan sada zumunta a yanar gizo cewa wai shima shugaban hukumar zaɓe Mahmood Yakubu ya fito takarar shugaban kasa.
” Ba zai taba yiwuwa ba, kuma ba za ayi ba, sgugaban Mahmood na INEC alkalin zaɓe ne kuma abinda ya saka a gaba ya kuma maida hankali a kai shine ya tabbatar da an yi sahihin zaɓe a 2023. Wannan shine a gaban sa.
Hukumar ta sanar ada haka a shafinta ta tiwita inda ta kara da cewa kogin takarar shugaban kasa ba na Mahmood bane, masu furta irin waɗannan kalamai ma su daina.
Saboda ganin arhar takarar a bana, wasu na ganin bari su yi wa shugaban hukumar tayi shima ya tsinduma kawai a fafata da shi.
Zuwa yanzu akalla sama da mutum 40 sun sayi fom ɗin takarar shugaban kasa a jam’iyyun APC, PDP, da sauran jam’iyyun kasar nan.
Discussion about this post