Gwamnan jihar Kaduna yayi sabbin naɗe-naɗe a jihar Kaduna.
Waɗannan naɗe-naɗe na kunshe ne a sanarwar da mai ba gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye wanda ya fitar ranar Talata a garin Kaduna.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Baba Bukar Alhaji a matsayin shugaban hukumar kididdiga ta jihar Kaduna, sai kuma Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, babban sakataren hukumar Alhazai ta jihar Kaduna, sai kuma Abdullahi Muhammad Ibrahim a matsayin mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa sai kuma Adama Abdullahi Wada a matsayin babbar Direkta na hukumar kula da ingancin makarantun jihar.
Adekeye ya ce dukkan su waɗanda aka nada kwararru ne a ɓangarorin su na karatu da ayyuka.
Discussion about this post