Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, wanda ke takarar gwamnan Jihar Kebbi, ya bayyana cewa ya inganta rayuwar sama da mutum 500 duk sun zama miloniya a Jihar Kebbi.
Malami ya bayyana aka a gidan sa da ke shiyyar hamshaƙan attajirai (GRA) a Birnin Kebbi.
Ya yi bayanin ne yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyoyin da ke goyon bayan takarar sa na neman zama gwamnan Kebbi a zaɓen 2023. Sun kai masa ziyarar ce a ciki makon da ya gabata.
Malami ya ce al’ummar Jihar Kebbi ne su ka matsa masa lambar cewa lallai ya fito takarar gwamna a ƙarƙashin APC. Dalili kenan inji shi ya amsa kiraye-kirayen da su ke yi masa.
Cikin makon da ya gabata ne Minista Malami ya yi watandar zabga-zabgan motoci 30 ga shugabannin APC da makusanta.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi watandar zabga-zabgan motoci masu tsada guda 30 ga makusantan siyasar sa da magoya baya a Jihar Kebbi.
Majiya ta tabbatar da cewa daga cikin manyan motocin da Malami ya rabas, akwai samfurin Marsandi GLK guda 14 waɗanda ya bayar ga ‘yan soshiyal midiya ɗin sa, ko kuma a ce sojojin baka, masu yaɗa manufofin neman takarar gwamnan Kebbi da Malami ke kan yi.
Ministan kuma ya raba wa sauran makusantan sa na siyasa motoci takwas samfurin Prado SUV’S, sai Toyota Hilux guda huɗu, sai kuma Lexus LX 57.
Wasu daga cikin waɗanda su ka ci moriyar motocin sun haɗa har da Mambobin Gidauniyar Malami, Ƙungiyoyin Mata Magoya bayan Malami.
An raba motocin ne kwana kaɗan bayan Malami ya bayyana aniyar sa ta fitowa takarar gwamnan jihar Kebbi.
Da ya ke jawabi lokacin bayyana fitowar sa neman gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin APC a zaɓen 2023 mai zuwa.
Duk da cewa Malami bai yi sanarwar raba motocin ba, amma dai hotunan motocin sun cika duniyar soshiyal midiya.
Sannan kuma Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Atiku Bagudu a Soshiyal Midiya, wato Zaidu Bala, ya taya waɗanda suka ci moriyar motocin murna a shafin sa na Facebook.
Sai dai kuma Umar Gwandu wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na Minista Malami, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa abokan arzikin Malami ne su ka sayi motocin su ka raba wa magoya bayan tafiyar siyasar sa, amma ba shi ne ya sayi motocin da kuɗin sa ya raba ba.
An dai ƙiyasta kuɗin motocin za su kai jimillar Naira miliyan 135.
Bayan yin watandar motocin ne Malami ya ce yayin da ya ke aikata alheri ga jama’a, wasu mutane kuma a can gefe ɗaya na ta yaɗa ƙarairayi a kan sa.
“Abin da na sani shi ne, waɗancan sun shafe shekaru su na ɓata ƙananan yara da muggan ƙwayoyi.
“Mu kuma mun maida hankali wajen tallafa wa dimbin matasa da samar masu aikin yi, domin mun samar wa sama da matasa 700 aiki ‘yan asalin Jihar Kebbi.
“Na gina sama da rijiyoyin burtsate 200 kuma na maida sama da mutum 500 sun zama miloniya a faɗin jihar Kebbi.”
“Mun samar wa sama da mutum 6000 tallafi korona na Naira 550,000, adadin kuɗaɗen da su ka kai Naira biliyan 3.2.” Inji Malami.