Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya bayyana cewa ba yabibiyan wani dan takarar shugaban Kasa ya nada shi mataimakin shugaban kasa.
Zulum ya kara da cewa babu wani dan takara da jihar tayi wa alkawarin za ta bashi kuri’un ta a zaben fidda gwani.
“Dalili kuwa shine mulki Allah ke bada shi saboda haka babu wani, duk wanda Allah ya ba shi ne za mu bi, amma mu ba mu isa mu ce ga wanda zai zama shugaban kasa ba dole.
” ‘Yan Najeriya sun shiga cikin matsi da tsananin gaske sannan ga tsantysagwaran talauci da ake fama da shi. Dole sai an maida hankali wajen kawo karshen haka za a cigaba da fama da wahalhalun da ake fama da su ne.
” Sannan kuma dole a maida hankali wajen yaki da cin hanci da rashawa. Ya kamata a dasuki wannan abu da mahimmanci ba da wasa ba. Shima akwao karshen sa. Idan aka yi haka ne kawai za a samu nasara da samun cigaba a kasar nan.
Rotimi Amaechi, wanda ya ke jihar domin neman goyon bayan wakilan jihar su zabe shi ya godewa gwamna Zulum sanna kuma ya ce idan ya zama shugaban Kasa zai fi maida hankali ne a fannin tsaro da kauda talauci a tsakanin al’umma.
Discussion about this post