Gwamnan Jihar Ekiti kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya ce a cikin ‘yan takara fiye da dozin biyu na APC, biyar ne kaɗai ke yi da gaske, sauran daga ‘yan rakiyar amarya sai burga kawai.
Ya ce mutum kamar 23 ne ke neman kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, amma mutum biyar ne kaɗai su ka nuna da gaske su ke yi shugabancin Najeriya ɗin su ke nema, kuma shi ne a gaban su.
Sai dai kuma Gwamna Fayemi bai ambaci waɗanda ke yin takarar da gaske ba. Kuma bai tantance ‘yan burga da ‘yan rakiyar amarya a cikin sauran ba.
Fayemi ya yi wannan iƙirarin lokacin da ya je neman goyon wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na Jihar Neja, a ganawar da ya yi da su a Minna, babban birnin jihar.
APC dai za ta yi zaɓen fidda gwani a ranar 29 da 30 Ga Mayu. Amma kuma har yau ba ta aza ranar da za ta tantance ‘yan takarar ba.
A ranar Lahadi ce APC ta fitar da sanarwar ɗage ranar tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar sai yadda hali ya yi.
Har yanzu dai ‘yan takarar sun bazu a cikin ƙasa su na ta kamfen ɗin neman goyon bayan wakilan zaɓen ‘yan takarar shugabancin ƙasa a jihohi daban-daban.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Fayemi mai suna Femi Ige ya fitar, gwamnan na Ekiti ya ce ana gane idan ɗan takarar shugaban ƙasa da gaske ya ke yi, ta hanyar ƙoƙarin sa wajen karaɗe dukkan jihohin ƙasar nan.
“Yanzu ne lokacin karaɗe jihohin ƙasar nan neman goyon baya. Akwai masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC har mutum 23. Amma mu biyar ne kaɗai ke ta karakaina a faɗin jihohin Najeriya.
“Kun ga a wannan ma’aunin kaɗai za ku iya tantance mu da ke yin takara da gaske, da kuma ‘yan rakiyar amarya da ‘yan burga.”
“Saboda haka ina neman goyon bayan ku. Na fito don na san na cancanta. Idan ku ka zaɓe ni, ba za ku yi da-na-sani ba.” Cewar Fayemi.
Discussion about this post