Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarci Kwamitin Dattawa da Amintattun PDP cewa su haɗa kai su tabbatar cewa PDP ta yi nasara a zaɓen 2023.
Atiku ya yi masu wannan kira ne a taron ganawar da ya yi da su ranar Talata a Abuja, inda ya nemi goyon bayan su don ganin an tsaida shi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, a zaɓen 2023 mai zuwa.
Ya ce zaɓen 2023 ya bai wa PDP damammaki masu yawa na samun nasara kuma jam’iyyar ta koma kan mulki.
“Amma kuma na damu sosai cewa idan ba mu haɗa kai muka ci zaɓen 2023 ba, to kenan fa za mu sake jiran yin adawar shekaru takwas kenan.
“Nan da shekara takwas kuwa ban san iyar waɗanda za su yi bankwana da siyasa ba. Sannan kuma hakan zai iya kashe jam’iyyar.
“Don haka wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga ci gaban rayuwar mu baki ɗaya. Ina so ku ƙara zama da natsuwa ku yi karatun ta-natsu.
“Yanzu ne lokacin da za mu tashi tsaye mu yi bakin ƙoƙarin mu. Ko dai mu yi ritaya tare, ko kuma mu yi nasara tare.”
Tsohon shugaban ƙasar ya ce mulkin PDP daga 1999 zuwa 2007 ya samar da ci gaba mai tarin yawa wanda har yau wata gwamnati ba ta samar da kamar sa a yanzu ba.
Ya ce PDP za ta ci ƙuri’u masu tarin yawa a zaɓen 2023, idan har Kwamitin Dattawa da Amintattun Jam’iyyar PDP ɗin su ka yi aiki tare, kafaɗa da kafaɗa.
“Wani ya ce mun samu ƙuri’u miliyan 12 a zaɓen da ya gabata. To ba ƙuri’u na ne Ni kaɗai ba ƙuri’un mu ne baki ɗayan mu.
Atiku ya ce shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki, 14 ɗan kudu ne shugaba, Obasanjo da Jonathan.
Discussion about this post