Marafan Kumasi da na Kasar Landan Alhaji Mohammed Sanusi Marafa ya yaba wa shugaban jami’ar MAAUN farfesa Adamu Gwarzo bisa huɓɓasan da yake wajen habbaka ilimi a Najeriya da Nahiyar Afirka.
A tattaunawa da yayi da Tubeless, Marafa ya ce irin tallafi da taimako da Farfesa Gwarzo yake baiwa waɗanda basu da karfi domin samun damar ilmantuwa abu ne da ya cancanci a yaba masa.
” A gaba na Farfesa ya baiwa wani matashi da matarsa tallafin karatu kyauta.
Wannan abu da yayi ya yi matukar faranta wa duk wanda ayke wannan wuri a lokacin da ake yi masa naɗin sarautar Wazirin Hausawan Turai.
” Haka kuma ko da na zo Najeriya na iske wasu da dama dake karatu kyauta wanda shine ya basu tallafi yin karatu ba tare sun kashe ko sisi daga aljihun su ba.
Marafa ya kara da cewa bayan zagaye da suka yi na duba jami’ar MAAUN Kano da suka yi ya roke farfesa ya garzayo Ghana ya zo ya buɗe jami’a irin haka.
” Mu fa ba ma sai ya kai girman jami’ar MAAUN ta Kano ba . Kuma ya yi mana alkawarin idan ya gama ya natsa zai duba hakan.
” Ina son in tabbatar muku cewa da za a samu irin farfesa Gwarzo 3 ko 5 a Najeriya da an warke daga matsalolin ilimi a Najeriya da Afrika baki ɗaya.
Discussion about this post