Bayan Shugaban Rasha Viladimir Putin ya gargaɗi NATO da Amurka cewa zai hargitsa Turai kakaf da yaƙi idan su ka kafa dokar hana jiragen sa kai hari Ukraniya, ƙasashen sun bayyana cewa ba za su shiga yaƙi da Rasha ba.
Babban Sakataren NATO Jens Stoltenberg ne ya bayyana haka bayan tashi daga taron gaggawa da ƙungiyar NATO ta yi, mai mambobi 30 a Brussels, babban birnin Belgium, ya ce “Mu NATO ba mu cikin yaƙin wannan rikici na Rasha da Ukraniya.”
Stoltenberg ya ce, “babban nauyi da haƙƙin da ke kan NATO shi ne mu tabbatar mun hana wannan yaƙi fantsama cikin ƙasashen Turai.
“Domin idan mu ka kafa dokar hana jiragen yaƙin Rasha shawagi a Ukraniya, to kenan za mu harbo duk jirgin Rasha da ya keta Ukraniya. Wannan kuwa zai janyo Rasha yin ramuwar-gayya kan ƙasashen Turai da dama. Hakan kuwa zai ƙara haifar da mumnunar asarar rayuka da dukiyoyi a Turai.”
‘Za Mu Taimaki Ukraniya Ta Kare Kan Ta, Amma Ba Za Mu Taya Ta Yaƙi Ba’ -Amurka
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinker ya bayyana cewa za su taimaka wa Ukraniya da dabarun kare kai, amma ba za su tare mata yaƙi da Rasha ba.
Blinker ya faɗi haka jim kaɗan bayan tashi daga taron Ƙasashen Ƙawancen NATO da su ka yi a Brussels, Babban Birnin Belgium.
‘Da kulki zan fasa ƙwalwar duk wani Waldima, Gogaji, Wargaji, ko Giji-gijin da ya nemi hana jiragen mu kai hari Birnin Ƙib da kewaye’ -Putin, Iliya Ɗanmaiƙarfin Rasha.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gargaɗi gungun ƙasashen Ƙungiyar Ƙawance Sojan Taron Dangi ta NATO cewa duk ƙasar da ta yi gangancin kafa dokar hana jiragen yaƙin Rasha kai hari Ukraniya, to ta sani ta shiga yaƙin kenan ita ma, saboda haka ‘maza bisa kan ta kawai’.
Putin ya ce ko kaɗan Rasha ba za ta saurara wa kowace ƙasar NATO ba, ko ita NATO ɗin kan ta, muddin su ka ce kada jiragen Rasha su keta hazon Ukraniya.
“Duk ƙasar da ta kafa mana dokar hana jiragen mu kai hari Ukraniya, to ita ma ta shigo yaƙin kenan. Kuma tsakanin mu da ita sai bata-kashi.” Inji Putin, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
A ɓangare ɗaya kuma, Shugaban Ukraniya ya caccaki ƙasashen Turai da Amurka da ke cikin NATO, saboda sun ƙi goya masa baya a yaƙin da ya ke yi da Rasha.
Discussion about this post